BBC na neman jami'in gudanarwar ayyukanta a Nigeria

Alamar BBC Hakkin mallakar hoto Getty Images

BBC na neman jami'in gudanarwa a Najeriya wanda zai jagoranci ayyukanta.

Ayyukan sun hada da kula da ma'aikata, da ayyukan yau da kullum, da kula da kudade.

Kuma zai tallafa wa ayyukan jarida a ofishinmu dake Abuja, ta hanyar shugabantar dukkan wadannan sassan da muka lissafa. Kana, shi ne zai gudanar da dukkan ayyukan da suka shafi ma'aikatan BBC a dukkan wuraren da BBC ta ke yin ayyukanta a Najeriya.

Domin cikakken bayani game da wannan aikin, duba wannan shafin:

http://careerssearch.bbc.co.uk/jobs/job/Operations-Manager-BBC-Abuja/21296

Ko wannan: https://goo.gl/97S6kF

Dukkan dan asalin yankin ECOWAS watau CEDEAO na iya neman wannan aikin.

Akwai damar yin tafiye-tafiye a cikin Najeriya, har ma da kasashen yankin Afrika ta Yamma da wasu sassan duniya ga wanda ya sami aikin.

Zamu gana da wadanda suka nuna sha'awar yin aiki da mu ranar 30 ga watan Yuni, 2017 a Abuja. Kuma muna bukatar wanda ya yi nasara ya kama aiki ranar Litinin 3 ga watan Yuli 2017.