'Nigeria za ta sha gaban Amurka wajen yawan al'umma'

Mutane a kasuwa a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Najeriya na da al'umma kusan miliyan 200

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya a kan yawan al'ummar Duniya na shekarar 2017 ya ce Najeriya za ta sha gaban Amurka a yawan al'umma..

Haka zalika rahoton ya yi hasashen cewa kasar za ta kasance ta uku mafi yawan al'umma a duk fadin duniya nan da shekarar 2050.

Rahoton wanda aka fitar a ranar Laraba ya ce a shekarar ta 2050 al'ummar duniya za ta kai 9.8 biliyan, kuma Indiya za ta wuce kasar Sin a yawan al'umma nan da shekaru bakwai masu zuwa.

A halin yanzu dai Najeriya ita ce kasa ta bakwai a yawan al'umma a duniya.

Rahoton ya bayyana cewa Najeriya ce kan gaba wajen habakar jama'a a cikin kasashen goma mafi yawan al'umma a halin yanzu a duniya.

Kun san shafin Facebook ɗin da matan Nigeria ke rububi?

'Za mu kai masu tuƙin ganganci asibitin taɓaɓɓu'

Tsutsa na cinye shukar manoma a Nigeria

Haka kuma a cikin kasashen goma mafiya yawan jama'a ita kadai ce a nahiyar Afrika.

Rahoton ya kara da cewa, a shekara ta 2050 yawan mutanen da ke cikin kowace kasa a cikin kasashe shida da ke cikin goma mafiya yawan jama'a zai wuce miliyan 300.

Kasashen su ne: Sin da Indiya da Indonesiya da Najeriya da Pakistan da kuma Amurka.

Rahoton ya nuna yadda yawan mutanen zai kasance - inda yace Indiya, wadda ta ke da mutane biliyan 1.3 za ta wuce kasar Sin mai mutane biliyan 1.4 nan da shekara ta 2024.

Rahoton ya kuma ce nahiyar Turai za ta fuskanci raguwar jama'a, kuma alkaluma sun nuna cewa yawan mutane masu shekaru sama da 60 za su ninka sau uku nan da shekarar 2100.

Labarai masu alaka