Coci ta 'hada baki' da bishop mai 'lalata' Peter Ball

peter ball Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An daure Ball kan laifukan lalata da ya aikata kan yara da matasa tsakanin shekarun 1970 da 1990

Wani bincike na mai zaman kansa ya gano cewar manyan limamai a Cocin Ingila sun hada baki da tsohon wani bishop wanda ya yi lalata da matasa.

An yi wa Peter Ball, wanda a yanzu ya ke da shekara 85, daurin wata 32 a watan Oktoban shekarar 2015 bayan ya amsa laifin yin lalata da yara da matasa 18.

Tsohon bishop din garin Lewes da Gloucester ya aikata laifin ne tsakanin shekarun 1970 da 1990.

Binciken da Dame Moira Gibb ta jagoranta ya soki tsohon babban limamin cocin Ingila, Lord Carey.

Ya amince da sukar kuma ya nemi gafar daga wadanda aika-aikar Ball ta shafa.

Binciken ya gano cewar Lord Carey ya karbi wasiku bakwai daga iyalai da kuma mutane daba-daban bayan an kama Ball kuma aka yi masa gargadi a shekarar 1992 domin aikata alfasha-a lokacin da ya sauka daga matsayinsa na bishop din Gloucester - amman ya kasa mika shida daga cikin waskun ga 'yan sanda.

Kuma ya ki ya saka sunan Ball cikin jerin sunayen wadanda ake tababa game da cancantarsu kan jagorancin majami'a.

An bai wa Ball kudade wadanda Lord Carey ba da damar bayarwa domin a tallafa masa.

Hakazalika Lord Carey ya rubuta wasika ga tagwai din Ball, Michael Ball - wanda shi ma wani bishop din ne - a shekarar 1993 inda yake cewa: "Na yi imanin cewar ba shi da laifi".

'Cutar da wadanda aka tozartar'

Babban limamin Cocin Ingila na yanzu, Justin Welby, ya nemi Lord Carey ya sauka daga mukaminsa na mataimakin bishop na girmamamwa a cikin gundumar cocin na Oxford.

Bishop din Oxford din,Reverend Dr Steven Croft, ya ce babban limamin Cocin Ingilan ya nemi Lord Carey ya yi masa magana.

A wata sanarwar da ya fitar ya ce: "Mun amince cewar za mu gana nan gaba domin wannan tattaunawar. A halin yanzu, ya yarda cewar zai janye daga filin ikilisiya."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lord Carey ya nemi gafara daga wadanda laifukan Peter Ball suka shafa

An saki Ball daga kurkuku ne a watan Fabrairu bayan shafe wata 16 a gidan yari.

Dame Moira, wadda tsohuwar jami'a mai kula da jin dadin jama'a, ta ce Coci ta nuna kasawa wajen mayar da martanin da ya dace ga arshin daiadan cikin shekaru da yawa.

A rahotonta mai taken "Yin amfani da addini domin son zuciya", Dame Moira ta ce: "Ball ya fi mayar da hankali ne kan kare kansa da kuma kuma ciyar da kansa gaba, amman ya cutar da wadanda aka tozartar.

"Cocin ta hada baki wannan maimakon ta nemi taimaka wa wadanda ya cutar ko kuma ba tabbacin amincin sauran matasa."

Binciken ya gano cewa "Abin da Ball ya aikata ya haddasa barna na din-dindin ga rayuwar mazaje masu yawa... Peter Ball ya yaudari cocinsa kuma ya tozartar mabiya cocin."

'Na yarda da Peter Ball'

A wata sanarwa, Lord Carey ya ce rahoton ba shi da dain karantawa.

"Na yarda da sukan da aka yi mini. Na nemi gafara wadanad laifin Peter Ball ya shafa."

Sanarwar ta kara da cewar: "Na yi yarda da martanin Peter Ball kuma na yardan da na nuna wa matasa da yaran da suka yi wannan zargin ya yi kadan."

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba