Al Jazeera ta mayarwa Ƙasashen Larabawa martani

Qatar Border Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya ta rufe kan iyakar ƙasa guda ɗaya rak da Qatar ke da ita

Kafar yada labaran Al Jazeera wadda take mallakin kasar Qatar ce ta mayar wa Kasashen Larabawa martani game da bukatarsu ta rufe gidan talabijin ɗin.

Ta ce bukatar da Kasashen Larabawan suka nema wani yunkuri ne na "hana 'yancin fadin albarkacin baki".

A wata sanarwa da Al Jazeerar ta fitar ta ce: "Mun yi imani da 'yancinmu na yin aikin jarida ba tare da ba da kai bori ya hau ba ga kowace gwamnati ko kuma hukuma."

Qatar na neman sulhu da kasashen Larabawa

Morocco za ta aike da kayan abinci Qatar

Amurka ta buƙaci a sassauta wa Qatar

A ranar Juma'a ne Ƙasashen Larabawa da suka katse hulɗa da Qatar a farkon wannan wata sun miƙa mata buƙata 13 da suke son ta cika.

Saudiyya da Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar sun nemi mahukuntan Qatar su rufe gidan talbijin na Al Jazeera.

Sun kuma ce ta rage hulɗa da ƙasar Iraqi sannan ta rufe wani sansanin sojan sama na Turkiyya duk a cikin kwana goma.

Kuwait wadda ke ƙoƙarin shiga tsakanin a rikicin ita ce ta damƙa wa Qatar jerin waɗannan buƙatu.

Haka zalika, ƙasashen na yankin Gulf sun nemi Qatar ta kwance duk wata alaƙa da ƙungiyar 'Yan'uwa Musulmi.

Ƙasashen dai sun zargi Qatar da samar da kuɗi ga harkokin ta'addanci, zargin da ƙasar ta musanta.

A farkon wannan mako ne ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce mamaki ya dabaibaye ta kan yadda ƙasashen ba su fitar da ƙarin bayani kan ƙorafe-ƙorafensu ba.