Tanzania: Hana 'yan mata masu ciki karatu ya jawo ce-ce-ku-ce

John Magufuli Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Magufuli ya ce 'yan mata masu juna biyu ba za su rika mayar da hankali ba a makaranta

Furucin Shugaban Kasar Tanzaniya, John Magufuli na cewa duk wata yarinyar da ta haihu ba za a barta ta ci gaba da karatu ba, ya janyo korafe-korafe daga 'yan kasar da dama.

Hakan ya kai ga har an fara tattara korafe-korafen ta intanet don neman shugaban ya janye kalamansa.

Mista Magufuli ya yi gargadin ne ga 'yan mata dalibai a ranar Litinin din da ta wuce: Inda ya ce "Muddin kika dauki ciki to taki ta kare ke nan."

A shekarar 2002 ne dai aka kafa dokar da ta amince a kori duk wata dalibar da ta dauki ciki a kasar.

Dokar ta ce za a kori yarinya daga makaranta saboda "laifukan da suka shafi rashin tarbiyya" da kuma "aure".

Korafe-korafen da ake tatara wa a dandalin sada zumunta na Twitter ya yi nuni da cewa, goyon bayan dokar da shugaban ya yi zai kawo karshen karatun 'yan mata da dama a kasar, kuma "zai janyo nuna bambanci."

Maimakon hakan an bukaci a bi hanyoyin da za su hana 'yan matan daukar cikin a yayin da suke karatu.

'Yan kasar Tanzania na sukar kalaman shugaban kasar tare da bayyana irin mawuyacin halin da 'yan mata ke shiga, a yayin da suka dauki ciki suna makaranta.

Makonni biyu da suka wuce ne dai mataimakin shugaban kasar, Samia Suluhu, ya yi kira da a mayar da 'yan matan da suka riga suka haihu makaranta, yana mai cewa bai dace a hana su damar samun ilimi ba.

'Daurin shekara 30 ga maza'

Mista Magufuli, wanda ke magana a wajen wani taron gangami a garin Chalinze da ke da nisan kilomita 100 daga yammacin birnin Dar es Salaam, ya ce 'yan matan da suka zama iyaye ba sa maida hankali a karatu idan sun koma makaranta:

"Da an fara darasin lissafi , sai ta ce wa malamin da ke ajinsu: Jaririna na kuka, bari na je waje na ba shi mama."

Shugaban kasar ya ce su kuma mazan da suka yi wa 'yan matan ciki, kamata ya yi a yi musu daurin shekaru 30 a gidan kurkuku, sannan a sa su aikin noma a lokacin da suke zaman jarun."

Shugaban ya kuma soki kungiyoyin kare hakkin bil'adama da ke matsa lamba a kan gwamnati sai ta janye dokar korar 'yan matan masu ciki daga makaranta:

"Kungyoyin su je su bude wa 'yan matan makarantu. Don ba za su tilasta wa gwamnati sai ta mayar da 'yan matan makaranta ba," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa "Ina ba da ilimi kyauta ga daliban da suka nuna cewa da gaske suke yi za su yi karatu, yanzu kuma kuna so in ilmantar da iyaye ne?"

Wakilin BBC, Sammy Awami, da ke Tanzania ya ce taron jama'ar da ke wurin sun rika tafa wa shugaban kasar yayin da yake jawabi.

Akalla 'yan mata 8,000 ne a kasar ke barin makaranta a duk shekara, saboda sun samu ciki, a cewar rahoton hukumar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba