Matar da ke taimakon marasa lafiya su mutu cikin sauki

Davaasuren da Renchin a asibitin Mongolia
Image caption Mongolia ta hada iyaka da kasashen China da Rasha

Shekara 15 da ta wuce babu abin da ake kira kula da marasa lafiyar da ke gaf da mutuwa a kasar Mongolia.

Sai dai a yanzu an samu hakan, sanadiyyar wata mata mai suna, Odontuya Davaasuren, wadda ta shawo kan cibiyoyin lafiyar kasar kan cewa yakamata a taimaka wa mutane su daina mutuwa a cikin azabar ciwo.

Mahaifin Odontuya Davaasuren ya mutu a Mongolia, bayan fama da cutar sankarar hanta a lokacin tana da shekara 17, kuma tana karatun kwarewa a fannin likitanci da ya shafi kananan yara a Leningrad da ke kasar Rasha.

"Ban samu damar kulawa da mahaifina ba ballantana mu yi sallamar karshe," in ji Odontuya.

"Lokacin da na dawo Mongolia, 'yar uwata ta shaida mini cewa mahaifinmu ya yi fama da tsananin ciwo."

Shekaru da dama bayan nan, lokacin da ta fara aikin likita kuma tana tare da surukarta wadda ke fama da cutar sankarar hanta, ta shaida yadda radadin ciwo ke hana mutane su mutu cikin sauki.

"Na kula da ita, na dinga ba ta abinci na wanke tufafinta na sauya mata kayan jikinta, amma duk da haka ban iya yin komai game da radadin ciwon da ke damunta ba don ban san yadda zan yi hakan ba," a cewarta.

Maganin da kawai ake da shi ga mutanen da ke gab damutuwa a Mogolia shi ne maganin ciwon jiki ko na ciwon kai, amma ba na radadin ciwon sanadin wani tsuro a ciki ba.

Babu wani magani da sauran cututtuka kamar na tashin zuciya da kuma amai.

"Na ji matukar kunya cewa ni ba likita ba ce ta gari domin ban san yadda zan taimaka ba," in ji ta.

Kamar hakan bai isa ba, a wajen aikinta ta sha ganin yaran da ke fama da amosanin jini suna cikin azabar ciwo ko iya murmushi ko magana ba sa yi.

Har ila yau, ta ga wata mata wadda ta dinga rusa kuka tana neman a kashe ta ko ta huta da tsabar azabar cutar daji na cikin ciki.

"Marasa lafiya da dama sun mutu a gida cikin tsananin ciwo na sarari da kuma na boye."

"A mafi yawacin lokuta iyalai kan koma kan maganin gargajiya wasu kuma na sayen magani masu tsada, sai dai duk da haka ba ta sauya zani ba."

Amma tsarin kulawa da mutanen da 'yan watanni ko wasu 'yan shekaru ne ya rage musu a duniya ko wata hanyar saukaka musu babu shi a Mongolia.

A lokacin da ta kai ziyara zuwa Sweden a shekarar 2000 domin halartar wani taron kungiyar masu ba da kulawa don sassauta yanayin ciwon da mutane ke ciki a nahiyar Turai ya sa ta gano bakin zaren.

Wanda ta hakan ne ta maida Mongolia kasar da ake saukaka mutuwa.

"Kafin na je taron na Stockholm a shekarar 2000, ban taba jin kalmar 'ba da kulawa don sassauci ba," in ji likitar.

"Don babu irin hakan a Mongolia ko wani yanki na al'umomin da ke bin tsarin gurguzu."

Da komawarta gida sai ta kai kukanta ga ma'aikatar lafiya ta Mongolia, amma kuma sai aka yi biris da ita.

"'Me ya sa za mu kashe kudade a kan mutanen da suka kusa mutuwa,' suka tambayeta 'yayin da ba mu da isassun kudaden kashewa marasa lafiyar da suke raye?'"

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Al'ummar kasar makiyaya ne a gargajiyance

Wata iska mai sanyi da za ta iya daskarar da yatsunka a cikin 'yan dakoki na kadawa a kan duwatsun da ke wajen Ulan Bator, babban birnin Mongolia.

Ba ka iya ganin gini ko daya ko fitilar kan hanya sai dai tanti da ake kira gers, wanda a gargajiyance makiyaya kuma manoma ke amfani da su.

Davaasuren wadda yanzu shekarunta 59 a duniya kuma tana da jikoki, ta shiga daya daga cikin tantin mai shudin kyaure na katako, inda ta hadu da Timurbat.

Yana jingine da bango a kan wani gado na katako, kuma a bayan gadon wani yadi ne mai adon furanni da aka kewaye jikin tanti da shi.

Marar Timurbat ta rabu gida biyu, fatarsa ta yi ruwan dorawa kuma idonsa ya zama ruwan goro a yayin da yake fama da cutar kansar hanta.

Image caption Cutar hanta kan yi wa mutum kisan mummuke ne

Timurbat ya kwashe tsawon rayuwarsa yana kiwon dabbobi akan doki, kamar dai wadanda suka gaba ce shi.

Amma a yanzu ko magana ma da kyar yake yi ballantana ma ya tsaya a tsaye.

"Kafafuna da hannuwana na yi mini ciwo, kaina na sarawa," yana magana yana runtse idanu.

"Bana iya bacci, ina ma ace bana jin wannan azabar ciwon."

Davaasuren ta tsuguna a gabansa ta taba cikinsa.

Ta ce "Kana iya ganin cutar kansar (cutar daji) a mararsa."

"Wannan matakin da cutar take babu magani sai dai zan so a ce baya jin azabar ciwon da yake ji a yanzu."

Har ila yau, ta tambayi matar Timurbat, Enkjargal, ko wane irin magani ake ba shi, inda ta bayar da shawarar a kara yawan maganin rage radadin ciwo na Morphine.

"A baya yana shan kwayar maganin daya a kowane sa'o'i hudu, amma a yanzu yana bukatar fiye da hakan don dayan baya isa," in ji likitar.

A wajen tantin yayin da Davaasuren ke shirin tafiya sai, Enkjargal ta fara zubar da hawaye.

Davaasuren ta rungume ta ta yi mata rada a kunne.

Kasar Mongolia kasar da aka fi mutuwa a sanadiyyar cutar kansa ko sankarar hanta - hakan ya rubanya sau shida irin yadda ake samun mutuwar a wasu kasashen duniya. - kuma alkaluman karuwa suke yi.

Ana kamuwa da kwayar cutar ne ta hanyar ciwon hantar ne nau'in B ko C.

Kuma yana yaduwa ne ta jini da saduwa (musammanma cutar nau'in B).

Fiye da kashi daya bisa hudu na mutanen Mongolia cutar ta yi musu mummunan kamu.

Cutar da kisa ne da sannu-sannu. Kuma a kan dauki shekaru cutar na cin hanta, sannan kuma ta janyo tsuro a jikin wasu masu fama da cutar.

Sai dai a lokacin da za a ga alamominta babu wani abin da za a iya yi.

"Mutuwa mai kyau... da kuma kyakkyawar rayuwa kafin mutuwa hakkin ne na dan Adam," in ji Davaasuren says.

Domin tabbatar da abin da take fada bayan komawarta gida, likitar ta dauki bayanan marasa lafiyar da suka kusa mutuwa a gida, inda ta dauki hoton bidiyonsu ta kai wa ma'aikatar lafiyar.

A wancan lokaci aka sallami marasa lafiyar da aka san sun kusa mutuwa daga asibiti ne su koma gida.

Kuma saboda ba su da maganin da zai rage musu radadin ciwon mafiya yawansu na kashe kansu ne.

"Mutane da dama na rokon in kashe su,'" a cewarta.

"Sun gwammace su mutu da su shiga wannan yanayin radadin ciwo. Bayan na dauki bidiyon ne sai na zauna da yamma in kalle su in yi ta kuka saboda ganin wuyar da suke sha."

Kuma saboda alkaluman da kasar ke da su na masu fama da cutar hanta, Davaasuren ta san iyalai da dama za su fada cikin wannan yanayi na ciwo.

Hakarta ta cimma ruwa ne a shekarar 2002, a lokacin da aka amince ta fito da wani shiri na sassauta zafin ciwo ga marasa lafiya domin taimakawa wadan da ke gaf da mutuwa da makusantansu.

Image caption Odontuya (a tsakiya) da wasu ma'aikatan jinya guda biyu

Bayan shekaru 15 kuma kowane asibitin lardin suna samar da wannan kular, haka ma dukkanin asibitoci tara da ke Ulan Bator.

Biyar daga cikinsu na bayar da kulawa ga marasa lafiyar da suka kusa mutuwa a asibiti da kuma a gida.

Wani sauyi da likitar ta kawo shi ne kara yawan maganin rage radadin da ake bayarwa.

Kafin ta taimaka wajen sauya dokar amfani da maganin ta kasa, mutane da dama sun yi imanin hakan zai kara sa wa a samu damar kara shaye-shaye.

Hakazalika, likitar ta bayyana cewa "A yanzu shagunan sayar da magani na iya rarraba maganin Morphine kyauta ga dukkannin masu fama da cutar hanta har zuwa mutuwarsa."

Ta kuma taimaka wajen bayar da horo ga dubban likitoci kan yadda za su bayar da maganin, sannan kulawa ta musamman ga marasa lafiyar da ke gadon mutuwa, tana mai cewa duka biyu suna da muhimmanci.

"Kulawa ta fannin addini ya fi shan maganin rage radadin muhimmanci," in ji ta.

"Irin wannan kulawar kan gusar da zafin ciwo yana kuma kwantar da hankalin marasa lafiya tare da kawar da fargabar da suke da ita da rashin bacci......kuma akwai yiwuwar su yarda da kaddarar da ta same su na mutuwa."

Image caption Likitoci na amfani da nau'rar zamani domin gano tsuro a cikin marasa lafiya

A dakin bayar da kulawar da ke babban asibitin kansa na Mongolia, Davaasuren na magana da wani mutum wanda fata ta kare masa da ke zaune a kan wani gado a kusa da taga.

"Sunansa Renchin kuma yana aikin gini ne a daji," Davaasuren ta yi karin bayani.

"Yana da 'ya'ya biyar, kuma yana cin cewa mutuwarsa ta kusa, sai dai a wasu lokutan idan 'ya'yansa na nan ya kan ce ya samu sauki kada su damu,"

"Amma yanzu na gaya masa lokaci ya yi da zai san abin da zai gaya musu da yadda zai gaya musu domin ina jin lokacinsa ya yi.

Gara a gaya musu gaskiya maimakon boyewa. Ya yi murmushi ba tare da ya yi kuka ba."

Likitar ta yi magana da 'yar Renchin wadda ke zaune nan kusa.

Dan murmushin da ke fuskatarta nan da nan ya gushe a yayin da suke magana, kuma kwalla ta fara zuba daga idanunta, sannan jikinta ya fara rawa.

"Na shaida mata cewa mahaifinta zai mutu," "Ta ce da tana da fatan zai iya warkewa, amma na shaida mata cewa cutar ta kai makura. Yanzu ba lokacin da za a yi ta dura masa magani ba ne lokaci ne da za ku nuna masa kauna. kuma ta ce ta gode ta fahimce ni.'

"Har yanzu abin na yi mini wuya, don a wasu lokutan ma tare da marasa lafiyar za mu yi ta kuka."