Yadda ake kammala azumin Ramadan a duniya

The moon Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana kawo karshen azumin watan Ramadan ne da sallar Eid al-Fitr, inda jama'a suke fitar da zakkar fidda kai da yin sallar idi cikin sabin tufafi.

Sai dai sanin takamaiman ranar da za a yi sallar abu ne mai wuya, kamar yadda da Ahmen Khawaja da Amir Rawash suka yi bayani.

Muhimmancin ganin wata

A yayin da watan azumin Ramadan yake zuwa karshe, galibin Musulmi biliyan daya da miliyan 800 suna fatan ganin jinjirin watan da zai kawo karshen watan azumi.

A addinin Musulunci ana amfani ne da tsarin kalandar hijiriya. Kuma watan Ramadan shi ne na tara.

A kowace shekara ana samun bambancin kwana 11 ne tsakanin kalandar da ta miladiya.

Amfani da lissafin kalandar hijiriya yana da matukar amfani ga Musulmi kuma daya daga ciki shi ne yadda ake lissafin watan Ramadan da ita a kowace shekara.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani kantin hijabi gabanin bikin Idi a birnin Jakarta

Musulmi suna azumtar watan Ramadan ne, inda suke kauracewa abinci da abin sha daga fitowar Al fijir zuwa faduwar rana.

Ana samun bambance-bambance nan da can a fadin duniya, inda wasu mutane a sansan duniya suke kwashe lokaci mai tsawo yayin azumi wasu kuma suke yin kankanin lokaci.

Ana amfani da tsarin kalandar ganin wata ne, wato a duk bayan shekara 33 ne yanayin da ake ciki yake koma yadda yake wato yanayin zafi ko na sanyi da sauransu.

Ana yin sallar Eid al-Fitr ne ranar daya ga watan 10 wato Shawwal.

Galibin Musulmi suna dogaro ne da sanarwar ganin watan da hukumomi suke ba su maimakon su duba watan da kansu.

Akwai wadanda suke amfani da na'urorin kimiyya don ganin watan. Har il yau, akwaiwasu da suke cewa su sai sun ga watan da idanunsu sannan za su dauka ko ajiye azumi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu Musulmi suna amfani da na'ura don ganin jinjirin watan Shawwal

Ba a yin ranar idi rana guda a duk fadin duniya, amma dai bambancin ba ya wuce na kwana daya ko biyu.

Misali, mahukunta a Saudiyya - kasar da galibi mabiya Sunni ne kuma nan ne addinin Musulunci ya samo asali. A can ana sanar da fara azumin ko ajiyewa ne bayan an tabbatar da ganin watan.

Galibin Musulmi da ke sauran kasashen duniya wannan tsarin suke bi.

Amma a kasar Iran, wadda galibin jama'arta 'yan Shia ne da kuma tsiraru mabiya Sunni, tana amfani ne da hanyoyi biyu - daya daga sanarwar Shugaban Addinin Kasar Ayatollah Ali al-Sistani, sai daya sanarwar daga malaman sunnin kasar wadda mabiya sunni ke bi.

A rana guda mabiya Sunni da takwarorinsu na Shia suka yi idin karamar sallah a shekarar 2016, karo na farko a shekaru masu yawa.

A kasar Turkiyya wadda ba ruwanta da addini, ana amfani ne da lissafin masana kimiyya don dauka ko ajiye azumi.

Sai dai a nahiyar Turai galibin mutane sukan jira sanarwa daga shugabannin al'ummarsu - kodayake hakan ya dogara ne da ganin watan wasu kasashe.