An kai harin ƙunar bakin wake Kamaru

BOKO HARAM Hakkin mallakar hoto Getty Images

An kai harin kunar bakin wake guda biyu a garin Mora da ke arewacin kasar Kamaru.

A safiyar ranar Juma'a ne wasu mutane ne da ake zaton 'yan Boko Haram suka yi kutse a garin.

Sai dai bayan jami'an tsaro sun gano su, daya daga cikinsu ya tada bam din da yake dauke da shi.

Hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa da dayan maharin da kuma wani mutum daya.

Akwai karin bayanin da Blama Malla tsohon dan Majalisar dokoki na yankin Mayo-Sava ya yi kan halin da ake ciki a yankin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Blama Malla yana bayani kan harin

Harin kunar-bakin wake a Kamaru

An kai hari kan barikin jami'an tsaro a Kamaru

A kwanakin baya ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a garin Bargaram.