An kama masu kitsa kai hare-hare biranen arewacin Nigeria

Nigeria Police Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sandan fari kaya suna aiki tare da 'yan sandan kayan sarki ne wajen tabbatar da doka da oda a Najeriya

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta kama wasu masu shirin kai hare-hare was birane a arewacin kasar.

Wata sanawar da Tony Opuiyo na hukumar ya fitar, ta ce hukumar ta bankado wani shirin kai hare-hare kasuwanni da wuraren shakatawa da kuma wuraren ibada a jihohin Kano da Sokoto da Kaduna da kuma Maiduguri.

Hukumar ta ce dakile harin ya biyo bayan kama wani mai suna Yusuf Adamu da Abdulmumini Haladu a Sokkwoto, wadanda ke shirin jagorantar kai hare-hare a Kano da safiyar Juma'a.

Sanarwar ta ce hukumar ta kama wani gwanin hada abubuwan fashewa, Bashir Mohammed a karamar hukumar Kumbosto da ke jihar Kano a ranar 20 ga watan Yuni inda aka samu bindigogi takwas kirar AK47 da gurneti 27 da harsasai 793 a gidansa.

Har wa yau an samu kwanson albarushi 20 cike da harsasai a gidan tare da komfutar tafi da gidanka uku, da wayar salula daya da kuma tukunyar gas.

Hukumar ta kara da cewar ta bankado shirin masu tada kayar bayan na shiga cikin jerin gwanon da 'yan shi'a ke yo a ranar tunawa da Birin Kudus.