'Miliyoyi ne ke fama da cutar amosanin jini a Nigeria'

Blood Pin Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Ana gadon cutar amosanin jini ce wadda ba ta maganin warkewa daga wajen iyaye

Wata matashiya da ke fama da cutar amosanin jini a Najeriya ta ce tana shiga mawuyacin hali a duk lokacin da ciwon ya tashi.

Ta ce sai dai a ɗauke ta, don kuwa ba ta iya tafiya, kuma takan shafe tsawon sa'a 24 tana murƙususu saboda ciwo.

Likitoci sun ce a yankin kudu da Hamadar Sahara, mutum miliyan 12 zuwa 15 ne ke fama da cutar amosanin jini kuma kashi sittin cikin 100 suna Najeriya.

Wani likita a babban birnin Najeriya, Dokta Ibrahim Kwaifa ya ce ba a san haƙiƙanin yawan masu cutar amosanin jini ba, amma dai ƙwararru na cewa mutum miliyan ashirin zuwa miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ita a duniya.

Haka kuma duk shekara ana haifar mutum kimanin 2,400 masu wannan cuta.

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Lafiyayyun ƙwayoyin halittun jini na da siffar ƙawanya, waɗanda suka nakasa kuma sukan tanƙware

Ya ce ana gadon cutar ne daga wajen iyaye masu halittun ƙwayoyin jinin da suka samu nakasa.

Matashiyar ta ce idan ciwon ya tashi: "Ba sassauci, zugi ko ta ina. Tun daga kaina har ƙarshen yatsuna na ƙafa.

Nakan ce a matsa min jikina, (amma) ko an matsa, ba amfani, sai dai in yi ta addu'a. Wani lokaci sai na shiga surutai da ba ma'ana saboda tsabagen ciwo"

Ta ce a wasu lokuta sai an kai ta asibiti don yi mata ƙarin ruwa da ba ta magunguna da za ta ji sassauci.

Ta ce ba shakka takan fuskanci ƙyama, musammam ta fuskar auratayya.

Hajiya Badiyya Magaji Inuwa mahaifiya ce da ke da 'ya'ya masu larurar amosanin jini kuma har ta kai ga kafa cibiya don tallafawa masu cuta.

Ta ce ta sanya kanta cikin sha'anin tallafa wa masu cutar ne saboda ta san irin raɗaɗin da suke ji.

"Irin magungunan da na ga yarana na sha don su zauna cikin ƙoshin lafiya su ne na ga ya kamata in dinga rabawa masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ba za su iya saye ba."

Ta ce amosanin jini, cuta ce da ke buƙatar shan magani har iyakar rayuwar mai fama da ita.

Kuma ta ce tana raba takardu ne na jerin magungunan da masu amosanin jini ke buƙata don samun tallafi daga mutane.

Dr. Ibrahim Kwaifa ya ce ta hanyar ɗaukar matakan wayar da kai da gwada nau'in jini a tsakanin masu niyyar yin aure ana iya guje wa haifar 'ya'ya cutar masu amosanin jini.

Labarai masu alaka