Ana fargabar ƙasa ta binne mutum 120 a China

Zaftarewar laka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana fargabar akwai gomman mutane da ƙasa ta binne sakamakon zaftarewar lakar

Masu aikin ceto a China na ci gaba da bincike don neman fiye da mutum 120 da ake fargabar wata gawurtacciyar zaftarewar laka sakamakon ruwan sama ta binne su.

Iftila'in ya faru ne a wani yanki mai cike da tsaunuka cikin lardin Sichuan daf da iyakar kasar da yankin Tibet.

Kimanin gidaje 40 ne suka lalace a ƙauyen Xinmo cikin yankin Maoxian, bayan wani ɓangare na wani tsauni ya rufta a cikin daren Juma'a.

Ma'aikatan ceto kimanin 400 ne suka duƙufa don lalubo masu sauran shan ruwa a gaba da duwatsu suka binne a cikin ƙasa.

Ana kokarin ceto mahaka ma'dinai a China

An hana China fataucin fatu da naman Jaki

Mun ga ribar haihuwa fiye da ɗaya — China

Hotunan da jaridar People's Daily ta wallafa sun nuna motocin buldoza na ƙoƙarin kawar da manyan ɓaraguzai da tarin ƙasa yayin da aikin ceto ke ci gaba.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An kai motocin haƙar ramuka don kwashe ɓaraguzai a ƙoƙarin zaƙulo mutane

An gano wasu ma'aurata da jaririnsu, inda aka garzaya da su asibiti bayan ma'aikatan ceto sun yi amfani da igiyoyi wajen kwashe manyan duwatsu, yayin da wasu ke binciken ɓaraguzai a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

A cewar kamfanin dillancin labaran China Xinhua zaftarewar lakar ta katse tsayin kilomita biyu na wani kogi.

'Yan sandan yankin sun ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a baya-bayan nan cikin yankin, kuma lamarin ya ƙara ta'azzara sakamakon rashin tsirrai a yankin.

Xinhua ya ce an rufe titunan yanki ga duk masu abubuwan hawa a ranar Asabar face ma'aikatan agaji.

Labarai masu alaka