Indiya: An kashe Musulmi 'don ya ci naman sa'

sa Hakkin mallakar hoto Getty Images

An kama wani mutum a kasar Indiya bisa zargin yana cikin gungun mutanen da suka kai wa wasu Musulmi hudu hari don sun ci naman saniya.

Mutumin wanda aka bayyana sunansa da Ramesh, an ce ya kai wa Musulmin hari ne ranar Juma'a yayin da yake cikin maye.

Daya daga cikin Musulmin ya rasu kuma an bayyana sunansa da Junaid Khan, mai kimanin shekara 16 da haihuwa.

Mabiya addinin Hindu suna martaba saniya kuma an haramta yankata a jihohi da dama da ke kasar.

An kashe Musulmi biyu kan satar saniya

Jagoran Musulmi a India ya rasu

Yayin da yake magana, Ramesh ya ce "abokaina ne suka ce na kai wa yaran Musulmin hari don sun ci naman saniya."

Mahaifin marigayin ya ce an kai wa yaran harin ne saboda kayan Musulmi da suke sanye da su.

Har ila yau, an ruwaito wani dan uwan marigayin yana cewa "maharan ba su ko kula da kalaman da yaran suke yi cewa su ba sa dauke da wani naman saniya."

Mabiya addinin Hindu su ne kashi 80 cikin 100 na jama'ar kasar Indiya, yayin da Musulmi suke kashi 14 cikin 100.

Labarai masu alaka