'Yan Nigeria su guji kalaman ta da hankali – Buhari

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karon farko kenan da aka ji muryar Shugaba Buhari bayan kwana 48

Shugaban Najeriya uhammadu Buhari ya nemi al'ummar ƙasar su guji maganganun tayar da hankali, su rungumi zaman lafiya da juna.

Ya ce "zama lafiya a Najeriya, shi muke roƙon Allah kullum."

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin saƙonsa na bikin ƙaramar sallah, karon farko bayan kwana 48.

Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya ce ga alama shugaban na bayani ne game da musayar kalaman nuna ƙiyayya "tsakanin wasu ɓangarori na Najeriya".

A iya fahimtata saƙon sahihi ne, murya ce ta Shugaba Muhammadu Buhari kuma murya ce wadda ta nuna an naɗe ta, ba da jimawa ba, in ji Tangaza.

Ya ce don kuwa ta yi bayani kan wasu batutuwa da ake ciki, da suka haɗar da bikin sallah da kuma damuna gami da uwa-uba kalaman nuna ƙiyayya.

A baya- bayan nan dai, Muƙaddashin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ta gudanar da taruka da wasu fitattun mutane da sarakuna don kwantar da ƙurar da ta taso.

Dambarwa ta ɓarke ne lokacin da wasu ƙungiyoyin matasa a arewacin ƙasar suka ba 'yan ƙabilar Igbo wa'adi na su fice daga yankin.

A cewarsu, saboda ƙaruwar kiraye-kirayen da wasu ƙungiyoyin Igbon ke yi don neman kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabas.

Lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da tankiya har ma da musayar ba da wa'adi a tsakanin wasu 'yan ƙasar.

A cikin jawabin, Buhari ya gode wa 'yan Najeriya kan yadda suke yi masa addu'o'in samun lafiya.

Ya kuma yi fatan saukar damuna mai albarka don samun abinci cikin sauƙi.

Ga Shugaba Buhari yayin da yake magana (sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don ku saurara)

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugaban Buhari yana takaitaccen jawabin barka da sallah ga 'yan Najeriya

Labarai masu alaka