Wani ƙwaro ya faɗa bakin shugaban ƙasa

Luis Guillermo Hakkin mallakar hoto @pzactual
Image caption Bayan ya taune rinar shugaba Luis Guillermo ya riƙa ƙiƙƙifta idanu

Shugaban ƙasar Costa rica, Luis Guillermo Solis ya taune ƙwaron da faɗa bakinsa lokacin da yake jawabi kai tsaye a wani taron manema labarai.

Shugaba Luis Guillermo na jawabi a gaban wasu 'yan jarida cikin makon jiya a garin Puntarenas, lokacin da wata rina ta yiwo shawagi daidai bakinsa.

Kuma kafin ya ankara, sai ta yi wuf ta faɗa ciki, shi kuma ya taune ta ya haɗiye.

Al'amarin dai ya ba wa mutanen da ke wajen tausayi da kuma mamaki, kuma ala dole aka dakata da jawabin har ya kurɓi ruwa.

An ji shugaban ƙasar a cikin bidiyon yana cewa na taune ta, na taune rina.

Hakkin mallakar hoto @pzactual
Image caption Bayan faruwar al'amarin shi da mutanen da suke wajen sun kece dariya
Hakkin mallakar hoto @pzactual
Image caption Luis Guillermo ya kwankwaɗi ruwa kuma ya ci gaba da hirar
Hakkin mallakar hoto @pzactual
Image caption Shugaban na Costa rica ya mai da al'amarin raha

Luis Guillermo ya riƙa ƙiƙƙifta idanu kamar zai yi amai amma ya dake.

Daga nan sai shi da 'yan jaridar da ke wajen suka kece da dariya har yana cewa: "ai wannan abinci ne mai gina jiki zalla."

Bayan shugaba Luis Guillermo ya sha ruwa kuma ya share bakinsa, sannan ya ci gaba da hira ga 'yan jaridar.