Masar ta sallama wa Saudiyya iko da tsibirai

Tiran da Sanafir Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tiran {na kusa) da Sanafir (na nesa) ba kowa a cikinsu sai sojoji da jami'an wanzar da zaman lafiya

Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da taƙaddama wadda ke miƙa ikon tsibiri biyu da babu kowa cikinsu a tsakiyar Tekun Maliya ga Saudiyya.

An cim ma yarjejeniyar sarayar da tsaunukan Tiran da Sanafir ne a lokacin wata ziyara da Sarki Salman ya kai Masar bara. Kuma majalisar dokoki ta mara mata baya a cikin makon jiya.

Batun ya haddasa zanga-zangar da ba kasafai ake yi ba a Masar, inda aka zargi shugaba Sisi da "sayar" da iyakar ƙasar don samun tallafin Saudiyya.

Sai dai, an ci gaba da tafka shari'ah kan matsayin tsibiran.

Wata kotun ƙasar ta soke shawarar miƙa wa Saudiyya tsibiran, yayin da wata kotun daban ta tabbatar da ita. Yanzu dai ana dakon hukuncin kotun tsarin mulkin Masar don ta yi nata hukunci a kan ɓangaren mulkin da ke da ikon ƙarshe a kan batun.

A cikin makon jiya ne, majalisar dokoki ta mara wa ƙudurin baya, inda ta ce tana da hurumi a cikin batun. Matakin da ya sake haddasa zanga-zanga a birnin Alƙahira.

Shugaba Sisi dai ya ce da ma can tsibiran mallakar Saudiyya ne, kawai dai ta nemi Masar ta jibge dakarunta ne a shekarar 1950 don kare su.

'Yan adawa sun zargi shugaban Masar ɗin da keta tsarin mulki tare da sallama iko da tsibiran da nufin daɗaɗa wa Saudiyya rai, wadda ke ba shi goyon baya na kuɗi tun lokacin da ya jagoranci juyin mulkin soja don kifar da zaɓaɓɓen magabacinsa, Mohamed Morsi a shekara ta 2013.

Image caption 'Yan adawa sun zargi shugaba Sisi da "sayar" da tsibiran waɗanda ke cikin teku ga Saudiyya
  • Sanafir da Tiran, tsibirai ne da ke kilomita huɗu a tsakani cikin Tekun Maliya.
  • Tiran yana nan a bakin mashigin ruwan Aqaba, a wani muhimmin ɓangaren teku da ƙasar Isra'ila ke amfani da shi wajen shiga Maliya
  • Babu kowa a cikin tsibiran face sojojin ƙasar Masar da dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙasashen duniya.
  • An jibge dakarun Masar ne a tsibiran tun a 1950, bayan Saudiyya ta nemi haka
  • Isra'ila ta ƙwace tsibiran a shekarar 1956 da 1967, daga baya kuma ta dawo da su ga Masar a lokutan biyu.

Labarai masu alaka