Kun san girman matsalar cutar kanjamau tsakanin ma'aurata?

Wani allon talla a birnin Abuja na Najeriya da ke jan hankali ga kare iyali daga kamuwa da HIV/AIDS Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aurata da dama ba sa gwaji saboda ba sa jin cewa suna fuskantar barazanar kamuwa da kwayar cutar HIV

Ƙasidar wannan makon ta duba yadda za a shawo kan cutar kanjamau yayin zamantakewar aure, da hanyoyin kiyaye yaduwarta tsakanin kishiyoyi da mai gida da kuma muhimmancin gwaji.

Kamar yadda aka sani, cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam da ciwon AIDS ko SIDA sun zama ruwan dare gama duniya.

Babbar hanyar da aka fi kamuwa da cutar ita ce ta jima'i.

Hakan ya sa wasu matan aure da ke da kishiyoyi kamuwa da cutar, saboda matan suna da miji guda ne wanda ke zagayawa daga wannan matar zuwa waccan matar daga lokaci zuwa lokaci.

Na san wata matar kirki wacce mijinta ya yi mata kishiya. Ita kishiyar tana da cutar kanjamau, amma ba ta bayyana wa mijin ba.

Bayan wasu shekaru, sai maigidan ya kamu da cutar, hakazalika ita matar.

Da ace mijin ya kai amaryar aka gwada ta a asibiti, da wannan mummunan al'amarin bai faru ba.

Abin takaicin shi ne dukkansu sun mutu a sanadiyyar cutar.

Wannan abu ne da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a cikin al'ummominmu, kuma ya dace mu dauki matakan kawar da wannan cuta da gaggawa.

A matsayin ki na matar aure, shin kina da yakinin samun cikakkiyar kariya daga kamuwa daga cutar kanjamau daga kishiyarki ta wurin saduwa da mijinki?

Sau nawa ya kamata ke da kishiyoyinki ku yi gwajin ciwon kanjamau a asibiti?

Akwai alfanu kuma abu ne mai karbuwa idan matar aure ta nemi ita da mijinta su rika zuwa wajen gwaji a asibiti tare.

Sai dai idan matar aure ta kamu da cutar, wadanne matakai ne za ta iya dauka?

Kuma yaya irin wannan al'amarin zai shafi zamantakewar aure a gidan da ke da kishiyoyi?

Kuna ganin yarje wa miji ko mata zai iya kare su daga kamuwa da wannan cutar?

Kuma yaya batun soyayya take idan aka gano akwai wannan cutar tare da wanda za a aura, ko wacce za a aura?

Abu na farko shi ne, idan mijinki yana son yin wani auren, shin za ki nemi mijinki ya kawo shaidar cewa matar da zai aura ba ta da cutar HIV mai karya garkuwar jiki?

Akwai alamar zaki samu goyon bayan mutane idan kika kafe sai an yi gwajin cutar HIV akai-akai?

Jami'an kiwon lafiya na kira ga mata da su tabbatar an gwada matan da mazajensu ke son su aura, kafin a daura auren.

Kana suna shawartan miji da matarsa su rika zuwa a gwada su akalla sau biyu a kowace shekara, idan suna son su tabbatar da ba su da cutar.

A yayin da nake tattaunawa da jami'an kiwon lafiya, na gane cewa wadanda ke dauke da cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam na iya samun rayuwa mai armashi tare da abokan zamansu.

Saboda irin ci gaban da aka samu a fagen samar da ingantattun magungunan da suke dakile habakar cutar a jikin masu fama da cutar.

An kai lokacin da matar da ke dauke da kwayar cutar HIV za ta iya haihuwar 'ya'yan da ba sa dauke da cutar.

Idan hakan ya ci gaba da wanzuwa, lallai zamu samu karfin gwuiwar a fatanmu na ganin karshen mummunar cutar nan ba da dadewa ba.

Kafin nan, ina kira da babbar murya a garemu duka da mu daina kyamar masu fama da cutar SIDA.

A maimakon haka, kamata ya yi mu rungume su kuma mu rika nuna masu kulawa da tausayawa.

Ba lallai ne wanda ya kamu da cutar ya zama ya samota ne ta hanyar banza ba.

Amma gaskiya lamarin shi ne masu wannan cutar marasa lafiya ne.

Kuma yana da kyau mu fahimci cewa ba a kamuwa da cutar ta hanyar gaisawa, ko runguma, ko kuma yin mu'amala da masu dauke da ita.

Wannan zai taimaka masu wajen gudanar da rayuwa mai amfani har ma su zama abin alfahari ga al'ummomin da suke tare da su.

Kirana ga kowa shi ne a rika gwada mu akai-akai, ko mai aure, ko mara aure domin ku san irin halin da kuke ciki.

Wannan ne zai taimaka muku, har da iyalanku wajen samun kariya daga kamuwa da wannan cutar.

Ga masu saurarenmu a rediyo akwai tattaunawa a kan batun da Dokta Habiba Ibrahim, da Alhaji Alwan Hassan (sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don ku saurara)

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Adikon zamani na wannan makon