Yemen ta faɗa annobar kwalara – MDD

A cholera-infected Yemeni receives treatment at a hospital amid a serious cholera outbreak in Sanaa, Yemen (22 June 2017) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Babu wani bangare na kasar Yemen da annobar ba ta kai ba, in ji Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Yemen tana cikim mummunar annobar amai da gudawa irin wadda ba a taba ganin irin ta ba a tarihin duniya, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

A wata sanarwa da hukumar Unicef da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka fitar sun ce yawan mutanen da suka harbu da cutar a kasar ya haura mutum 200,000.

Kawo yanzu mutum 1,300 ne suka mutu - daya bisa uku na wannan adadin yara kanana ne - yayin da ake ganin yawan wadanda suka mutu zai ci gaba da karuwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana daukar matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.

"Muna fuskantar mummunar annobar kwalarar da duniya ba ta taba ganin irin ta ba," in ji sanarwar.

Ta ci gaba da cewa: "A cikin wata biyu kacal, cutar ta karade duka fadin kasar Yemen wadda yaki ya daidaita."

Ana samun rahoton sabbin kamuwa da cutar kwalara kimanin mutum 5,000 a kowace shekara a Yemen.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Annobar ta fi shafar yara kanana

Fannin kiwon lafiyar kasar ya gurkushe yayin da ake fuskantar karancin ruwa saboda shekara biyu da kasar ta yi a cikin yaki.

Kawancen da Saudiyya ke jagoranta ne yake mara wa dakarun gwamnati Yemen baya a yakin da suke da 'yan tawayen Houthi.

Babban birnin kasar Sanaa da sauran garuruwan kasar suna karkashin ikon 'yan tawayen ne.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba