Zai yi wahala Qatar ta cika sharuɗan da su Saudiyya suka sanya wa Qatar -– Amurka

Border crossing with Saudi Arabia
Bayanan hoto,

An rufe kan iyakar Qatar da kasashen hudu

Amurka ta ce wasu daga cikin sharuɗan da kasashen Larabawa huɗu suka sanya wa Qatar kafin su janye takunkumin da suka aza mata za su yi wahalar cikawa.

Sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson, wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa amma sharudan sun bayar da wata kafa da za ta sa a samu mafita ga rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.

A ranar Asabar, ministan harkokin wajen Qatar ya yi fatali da sharuda 13 da Saudiyya da kuma kawayenta wadanda suka hada da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain suka gindaya wa kasarsa.

Sun zargi Qatar da goyon bayan ta'addanci - zargin da ta musanta.

Qatar ta fada cikin ce-ce-ku-ce na diflomasiyya da takunkumin karya tattalin arziki fiye da mako biyu da suka wuce, inda Iran da Turkiyya ke kai mata kayan abinci da sauran kayan more rayuwa.

Kasashen hudu na son cikin kwana goma Qatar ta janye dangantakar da ke tsakaninta da Iran sannan ta rufe sansanin sojin Turkiyya da ke kasarta.

Cikin sharudan da aka gindaya wa Qatar, har da rufe gidan talabijin na Al Jazeera, wanda kasar ke gudanarwa.

Mr Tillersonya ce Qatar na yin nazari kan bukatun da aka sanya mata, yana mai cewa hakan ya nuna cewa an "soma gano hanyoyin yin sulhu".

Ya yi kira ga kasashen su zauna tare domin kawo karshen ta'addanci da 'yan ta'adda.