'Yan sanda sun hana taron 'yan luwaɗi a Turkiyya

'Yan sandan Turkiyya sun cafke wata mata da tsare ta a lokacin taron masu goyon bayan auren jinsi guda Parade Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shekara uku kenan hukumomin kasar Turkiyya na hana gudanar da taron

'Yan sanda a kasar Turkiyya sun hana gudanar da wani haramtaccen taro da masu auren jinsi daya suka shirya.

Masu shirya taron a duk shekara, sun sha alwashin ci gaba da fafutuka da matsa lamba har sai sun cimma nasara duk kuwa da cewa hukumomin kasar ne suka haramta shi, wadanda ke fuskantar matsin lamba daga masu ra'ayin mazan jiya.

A kasar Turkiyya, an haram ta luwadai da madigo ba kamar wasu kasashen musulmi ba, amma duk da haka masu wannan ra'ayi na ci gaba da matsa lambar halatta shi.

Shugaba Tayyip Erdogan, wanda jam'iyyar sa ta 'yan mazan jiya kuma masu ra'ayin addinin musulunci ce, ya ki amincewa da bukatar tasu, da kin amincewa a sanya harkokin addinin gargajiya cikin kundin tsarin mulkin kasar, sai dai ya bai wa 'yan kasar damar gudanar da addinan da suke yi cikin bainar jama'a ba tare da tsangwama ba.

Sai dai ana zargin shi da karawa kan shi karfin iko cikin shekarun da suka wuce.

Har an saba da hakan

Wannan shi ne karo na uku cikin shekara uku ana haramtawa 'yan luwadi gudanar da babban taronsu a Turkiyya.

Wakilin BBC Mark Lowen da ke birnin Santambul ya ce irin jami'an 'yan sanda da aka jibge a titin yankin Istiklat ya haramtawa masu gangamin fara taron anan wanda daman nan aka shirya fara shi.

Ya kara da cewa duk wanda ya daga tuta launin bakan gizo, tare da kokarin wucewa ta wurin 'yan sanda na hana shi.

Haka kuma 'yan sanda dauke da makamai, da feshin ruwan da ake yi wa masu macin shi ya tilasta musu ja da baya.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu tattakin sun ce su na mutunta kundin tsarin mulkin kasar

Jaridar Hurriyet ta rawaito akalla mutane 10 ne ake tsare da su.

Yayin da jaridar De Telegraaf ta kasar Hollan, ta wallafa a shafin ta na Twitter cikin wadanda ake tsare da su har da mai daukar hoton ta Bram Janssen.

Tun da fari a jiya Lahadi, masu shirya macin goyon bayan 'yan Luwadi suka fitar da wata sanarwa mai taken: "Mu ba matsorata ba ne, ba za mu sauya ba, ba kuma inda za mu je, ku ne matsorata, za ku sauya, za kuma ku saba da hakan. Mun sake fitowa don nuna muku za mu yi fito-na-fito da duk wanda ke son danne mana hakkinmu."


Labarai masu alaka

Karin bayani