PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya ce babu wani bambanci tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da kuma jam'iyyar adawa ta PDP a kasar.

Sai dai tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ta'annati (EFCC) ya ce da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki da cin hanci da rashawa.

Malam Nuhu shaida wa BBC cewa kudaden da ake kwatowa da wurin barayi da kuma gurfanar da su da ake yi a gaban kuliya sun nuna cewa gwamnatin Buhari ta kama hanyar kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya.

A cewarsa, "Gwamnati na kokari matuka. Da ma niyya ake so mai kwari; idan aka samu shugaba na gari wanda ya ce ba ya son cin hanci, to za a samu mafita.

Sannan an karbe dukiyoyin da aka sace. Idan ka je babban bankin Najeriya za ka ga kudin da aka kwato. Wannan aiki ne na bangaren zartarwa".

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
PDP da APC abu daya ne - Nuhu Ribadu

Tsohon dan takarar shugaban na Najeriya ya roki sauran bangarorin gwamnati - alkalai da majalisa - sun zage dantse wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Ya ce lokacin da yake jagorancin EFCC, an kama mutane da yawa kuma an hukunta su, yana mai yin watsi da zargin da ake yi masa na cewa ya zama karen farautar tsogon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo inda ya rika tuhumar masu adawa da waccan gwamnatin.

"Na sha kalubalantar mutane cewa su kawo hujjar cewa ina zabi ɗai-ɗai a yakin da nake yi da cin hanci amma har yanzu ba su kawo ba. Kar ka manta akasarin mutanen da na sa aka daure a wancan lokacin 'yan jam'iyyar PDP ta tsohon shugaban kasa ce".