Nigeria: Mutum 19 ne suka mutu a harin Maiduguri

An sha kai hare-hare a Jami'ar Maiduguri Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption An sha kai hare-hare a Jami'ar Maiduguri

Akalla mutum 20 ne suka mutu bayan wasu 'yan kunar bakin wake sun tashi bama-baman da ke jikinsu a Jami'ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

A ranar Lahadi ne 'yan kunar bakin wake suka tashi bama-baman da ke jikinsu a Jami'ar Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar maharan da ma wata ma'aikaciyar Jami'ar.

Kakakin Jami'ar Farfesa Danjuma Gambo ya shaida wa BBC cewa maharan sun tashi bama-baman ne a wuri uku.

"Mace ta farko ta tunkari jami'an tsaron da ke aiki a jami'ar ne inda ta tayar da bam din da ke jikinta. Daya daga cikin jami'an tsaron ta mutu sannan an kai uku asibiti. Ta biyu kuma ta shigo ta gabashin Jami'ar amma jami'an tsaro suka gan ta, nan take suka harbe ta. Bam na uku kuma ya tashi ne a can nesa da jami'ar don haka ba mu sani ba ko mace ce ko namji suka yi yunkurin kai harin".

Farfesa Gambo ya ce hukumomi na ci gaba da tsaurara matakan tsaro a Jami'ar, yana mai cewa ana kai irin wadannan hare-hare ne saboda girman da Jami'ar ke da shi kuma ba a katange dukkanta ba.

A wannan shekarar dai an sha kai hare-haren kunar bakin wake a Jami'ar ta Maiduguri, abin da wasu ke ganin na da nasaba da rashin inganta tsaro a Jami'ar, ko da yake hukumomin tsaron na cewa suna yin bakin kokarinsu.

Labarai masu alaka