Trump ya ki shiryawa Musulmi liyafar sallah

US President Donald Trump talks with Secretary of State Rex Tillerson at the White House on 12 June, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai rahotannin da ke cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson (daga hagu) shi ne ya ki amincewa da bukatar shirya liyafar

Shugaban Amurka Donald Trump ya ki yin liyafar sallah a fadar White House kamar yadda sauran shugabannin Amurka da suka gabace shi suka saba yi.

Bana shekara 20 ke nan da tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton ya fara shiryawa Musulmi liyafar sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.

Bikin sallahar idi shi ne yake kawo karshen watan azumin Ramadan.

Tun daga zamanin Clinton ne aka ci gaba da raya al'adar shiryawa al'ummar Musulmin Amurka liyafar cin abinci har zuwa bara zamanin Shugaba Barack Obama.

Rahotanni na cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ne ya ƙi amincewa da bukatar shirya liyafar cin abincin.

A watan Mayu kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Mista Tillerson ya ƙi amincewa da wasu buƙatocin ma'aikatar harkokin wajen Amurka kan al'amuran da suka shafi addinai.

Ana sukar Mista Trump saboda yadda yake yawan bayyyana kalaman kin jinin Musulmi ciki har bukatarsa ta hana wasu Musulmi shiga kasar.

Kodayake Shugaba Trump ya aike da sakon sallah, inda ya ce: "Amadadin Amurkawa da mai dakina Melania da kuma ni kaina ina taya Musulmi murnar bikin Eid al-Fitr.

Sai dai shugaban bai yi karin haske ba game da abin da ya sa fadarsa ba ta gayyaci Musulmi liyafar ba.

Hana musulmi shiga Amurka, wariya ce?

Bahaushe ya zama kansila a Amurka

Trump ya zama 'saniyar ware' kan dumamar yanayi

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Duk shugabanin da suka biyo bayan Clinton sun rika shirya Musulmi liyafar ciki da Barack Obama a bara

Shugaban Amurka Thomas Jefferson ne a shekarar 1805 ya fara shiryawa Musulmi liyafar buda baki a fadar White House lokacin azumin watan Ramadan.

A shekarar 1996 ne uwargidan Shugaban Amurka Bill Clinton wato Hillary ta fara raya wannan al'adar.

An rika gudanar da liyafar ne kowace shekara daga shekarar 1999, inda shugabannin al'ummomin Musulmi a Amurka da masu aikin diflomasiyya da kuma 'yan majalisa suku halarta.

Labarai masu alaka