El Hadji Diouf: Ni ba mutumin banza ba ne

El Hadji Diouf
Image caption El Hadji Diouf yana zaune yanzu a kasar Senegal ne

El Hadji Diouf wani gwarzo ne a kasar Senegal. Duk wurin da ya taka kafarsa jama'a magoya bayansa yara da manyan ne suke kewaye shi. 'Yan kasar ba sa mantawa da muhimmiyar rawar da ya taka a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002, wanda kasashen Japan da Koriya ta Kudu suka karbi bakunci.

Amma a kasar Ingila, ana tunawa da shi ne kan yadda ya rika jawo ce-ce-ku-ce fiye da gogewarsa a fagen wasan tamaula.

Tsohon dan wasan ya yi wasa a kungiyoyi da dama ciki har da Liverpool da Blackburn Rovers da Bolton Wanderers da kuma Rangers ta yankin Scotland.

Diouf yana da saurin fushi, yana tasamma abokan wasansa da jami'an wasa.

Sai dai yanzu da ya yi ritaya, ya ba da labarin abin da ya faru.

'Bana daukar kaddara'

"Zaki nake, bana daukar kaddara kuma babu wata matsala idan mutum ya kasance haka," in ji Diouf yayin da yake magana game da halayyarsa lokacin da yake wasa.

"Ina da dabi'u masu kyau kuma ina so mutane su kaunace ni."

Diouf wanda ya koma babban birnin Senegal, Dakar, ya ce mutane ba sa fahimtarsa lokacin da yake wasa a Ingila.

Ya ce: "Ni ba mutum ne mai sauki ba. Yana da sauki a yi maganar El- Hadji Diouf kuma ina barin mutum ya fadi albarkacin bakinsa, amma ni na san cewa ni mutumin kirki ne. Iyalina sun san haka, jama'a sun san haka, nahiyata ta san cewa ni mutumin kirki ne, hakan shi ne abin da ya fi min komai. Sauran babu abin da ya sha mini kai."

Duk da yadda ya rika kare kansa, Diouf ya ce ya yi wasu dabi'u da ba su dace ba.

Da aka tambaye shi me ya sa, misali, yadda yake tofa wa takwarorinsa 'yan wasa yahu, ya ce: "Wata kila suna fada mini wani abu ne da bana kaunar ji. Na yi haka, na biya kuma yanzu na gama."

'Gerrard bai taba yi wa kasarsa komai ba'

Diouf ba ya jituwa da wasu daga cikin takwarorinsa a Liverpool kamarsu Jamie Carragher da kuma Steven Gerrard.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Steven Gerrard da Diouf sun yi wa kungiyar Liverpool wasa tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004

Ko yanzu, Diouf da Gerrard sun ci gaba da takaddama da juya ta kafafen yada labarai. Mene ne asalin matsalar?

"Ba ni da wata matsala da shi," in ji Diouf. "

"Gerrard yana da tasiri sosai kuma ni ma ina da tasiri sosai. 'Stevie G' dan wasa ne mai kyau. Mutane suna kaunarsa sosai a Liverpool amma bai taba yi wa kasarsa komai ba. Ni ne Mista El Hadji Diouf, Mista Senegal amma shi shi ne Mista Liverpool kuma Senegal tafi Liverpool kuma ya kamata ya san haka."

Diouf yana aiki ne a Senegal a matsayin jakada. Kuma shi ne yake bai wa Shugaban Senegal Macky Sall shawara kan wasanni kuma yana tafiyar da wani kamfanin jaridar wasanni a birnin Dakar - gungun mutane suna kewaye shi duk lokacin da ya je wurin motsa jiki.

"Rayuwata ta wasanni ce amma gwamnati ba za ta iya komai ba ita kadai, tana bukatar taimako daga mutane irina," in ji Diouf.

"Shugaban kasa ya yi amanna da ni kuma wannan ne ya sa da na yi ritaya daga wasa sai ya kirani ya ce yana so na taimaka saboda yaran da ke tasowa sun yi amanna da ni. Ni wani babban misali ne a gare su."

Hakkin mallakar hoto El Hadji Diouf
Image caption Diouf ne mashawarcin Shugaba Macky Sall kan wasanni

Da aka tambaye shi ko yana da burin shiga siyasa, Diouf ya ce ya mayar da hankalinsa wajen ganin ya bunkasa kasarsa - amma ba zai kore yiwuwar shiga siyasa ba a nan gaba.

Ya ce: "Ina da sha'awa saboda sai mun sauya al'amura. Mutane irina za su iya sauya al'amura."

"Muna da kasar da muke so mu gina da kuma nahiya, to me zai hana mutum shiga harkokin siyasa a gobe?"

'Mun sanya Senegal a sahun kasashen duniya'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002 ne ya kara fito daga Diouf (wanda yake tsakiya)

Sau biyu yana lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Afirka, Diouf yana cikin tawagar kasar Senegal da ta kai wasan kwata final a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002, a cikin kasashen da suka doke har da kasar Faransa.

Ya bayyana lokacin da kololuwar nasarar da ya samu a matsayinsa na dan wasa - yana kwatanta rawar da ya taka da wadda Diego Maradona ya taka yayin da Argentina ta lashe Kofin Duniya.

"Mun sanya Senegal a sahun kasashen duniya," in ji. "Gabanin wasan Kofin Duniyan babu wanda ya san da kasar Senegal, amma bayan wasan Kofin Duniya kowa yana ya san inda take."

"Abin da Maradona ya yi wa kasarsa, ni ma shi ne abin da na yi wa Senegal. Ina daya daga cikin manyan 'yan wasa a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002."

"Faransa ce ta yi mana mulkin mallaka. Gabili su ne suke tafiyar al'amura a Senegal saboda haka doke su da muka yi a gasar, ba karamin abu ba ne."

"Kafin wasan sun ce ba za su sanya manyan 'yan wasansu ba saboda galibin 'yan wasan sun yi wasa a lig din Faransa."

"A lokacin ni ina Lens, Salif Diao yana Sedan, Khalilou Fadiga yana Auxere, galibin 'yan wasan suna wasa ne a Faransa amma mun sha fadin cewa: 'A bi a hankali kafin a kashe zaki.'"

Diouf ya ce yana so ya ci gaba da taimakawa wajen bunkasa kwallon kafa a nahiyar Afirka, amma ya ce akwai bukatar sauya tsare-tsaren da ake da su yanzu.

"Hukumar Fifa ta sauya don haka lokaci ya yi da Hukumar Kwallon Kafar nahiyar Afirka ita ma za ta sauya," in ji shi.

Labarai masu alaka