Kotu ta amince Trump ya hana Musulmi shiga Amurka

Protesters at Los Angeles International Airport on 4 February 2017 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane sun yi ta zanga-zanga lokacin da aka hana Musulmi zuwa Amurka a watan Janairu

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke wanda ya ba shi damar hana Musulmi daga wasu kasashe shiga kasar, yana mai cewa hakan "wata nasara ce ga tsaron kasa".

Kotun kolin ta kuma amince da wani bangare na bukatar fadar White House ta hana 'yan gudun hijira shiga kasar.

Alkalan kotun sun ce a watan Oktoba ne za su yanke hukunci na karshe kan ko za a bai wa shugaban kasar damar hana Musulmin shiga Amurka kwata-kwata ko kuma za a yi watsi da bukatar tasa.

Mr Trump ya bukaci hana Musulmi kasashe shida shiga Amurka na kwana 90 nan take da kuma hana 'yan gudun hijira shiga kasar na kwana 120.

Shugaban na Amurka ya yi marhabin da hukuncin kotun na hana masu kai ziyara kasar daga kasashen Iran, Libya, Somalia, Sudan, Syria da Yemen, wadanda ya bayyana a matsayin kasashen "da ke da kyankashe 'yan ta'adda".

"A matsayi na na shugaban kasa, ba zan bari mutanen da za su yi mana illa su shigo kasar nan ba," in ji shi.

Tuni dama Mr Trump ya ce dokar za ta soma aiki cikin kwana uku bayan amincewar kotun.

Me kotun ta ce?

Abin da hukuncin kotun kolin na ranar Litinin ke nufi shi ne: "A aikace, hakan na nufin [ikon shugaban kasar] ba zai hau kan 'yan kasashen waje wadanda ke da kwakkwaran dalili na wata dangantaka da mutum ko kungiya da ke zaune a Amurka ba.

"Dukkan 'yan kasashen waje na fuskantar yiwuwar gamuwa da ikon da shugaban kasar ke da shi."

Hukuncin ya amince a hana dukkan 'yan gudun hijira shiga Amurka tsawon kwana 120, don haka za a bai wa gwamnati damar hana masu ikirarin gudun hijira wadanda ba su da wani dan uwa ko kungiya da ke zaune kasar damar shiga kasa.


Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wata 'yar kasar Yemen rungume da mahaifiyarta a filin jirgin saman Virginia a watan Fabrairu bayan kotu ta dakatar da Shugaba Trump daga hana Musulmi shiga kasar

Labarai masu alaka