Amurka ta gargadi Syria kan hari da sinadari mai guba

A man breathes through an oxygen mask as another one receives treatments, after what rescue workers described as a suspected gas attack in the town of Khan Sheikhoun in rebel-held Idlib, Syria April 4, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sinadari mai guba ya kashe fiye da mutum 80 a lardin Idlib a watan Afrilu

Amurka ta ce ta gano wani shiri da gwamnatin Syria ke yi na kai hari da sinadari mai guba kuma ta gargade ta kan hakan.

Fadar White House ta ce shirin da Syriar ke yi ya yi kama da wanda ta yi gabanin harin da ta kai da sinadari mai guba a watan Afrilu.

Mutane da dama ne suka mutu a wancan harin, lamarin da ya sa shugaban Amurka Donald Trump ya yi gaggawar bayar da umarni a kai hari kan sansanin sojin saman Syria.

Amurka ta yi gargadin cewa Shugaba Bashar al-Assad zai "yi matukar da-na-sani" idan kasarsa ta sake kai hari irin wancan.

Sanarwar da fadar ta fitar ta ce "harin sinadari mai guba da gwamnatin Assad za ta sake kai wa" zai iya haddasa kashe dubban farar-hula.

"Kamar yadda muka fada a baya, Amurka ta shiga Syria ne domin kawar da kungiyar IS da ke Iraqi da Syria. Idan Mr Assad ya sake yin amfani da makami mai guba ya kashe dubban mutane za mu kai masa farmakin soja, " in ji sanarwar.

Shugaba Assad ya musanta cewa dakarun kasarsa ne suka kai wancan harin a garin Khan Sheikhoun da ke lardin Idlib.

Farar-hula da dama, ciki har da yara da yawa ne suka mutu.

Jiragen ruwan Amurka da ke jibge a kogin Meditareniyan sun mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami samfurin Tomahawk guda 59 a kan sansanin sojin saman Syria na Shayrat wanda ke yammacin birnin Homs, inda aka ce a can ne ake ajiye makamai masu guba.

Labarai masu alaka