An ci zarafin mata Musulmi a Poland

Muslim girls, file pic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan matan Musulmi sun yi mamakin wannan wariya

'Yan mata Musulmi 'yan wata makarantar Jamus da suka kai ziyara wuraren da ake ajiye kayan tarihin tunawa da kisan kiyashi a gabashin Poland sun ce mazauna yankin sun nuna musu wariyar launin fata.

Matan, 'yan makarantar birnin Berlin, sun shaida wa gidan rediyon Deutschlandfunk abubuwan da suka fuskanta lokacin ziyarar. Hudu daga cikinsu suna sanye da hijabai kuma sun ce an ci zarafinsu.

Wata daga cikinsu ta ce wani mutum ya tofa mata yawu a kan titin Lublin, yayin da 'yan sanda ke tsaye suna kallo suna kuma murmushi ba tare da sun dauki mataki ba.

'Yar uwarta kuma ta ce an kore ta daga wani kantin sayar da kaya saboda ta yi magana da harshen Fasha.

A lokacin, magana take yi da dan uwanta a wayar tarho.

Ta gaya wa gidan rediyon cewa, "Masu kantin sun zo wurin da nake suka ce 'ki tafi ki bamu wuri domin kina damun mutane'. Don me suka yi min haka? Kawai saboda na yi magan da harsahen Fasha kuma ni 'yar kasar waje ce."

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Lublin ta fitar ranar Talata ta ce "matan ba su kai wani korafi ga jami'an 'yan sandan Lublin ba".

Cibiyar tunawa da kisan kiyashin Jamus ce dai ta dauki nauyin ziyarar da matan suka kai Poland.

Shugabanta Hans-Christian Jasch ya ce : "Na yi matukar girgiza da jin abin da ya faru da 'yan matan da muke kula da su a lokacin ziyarar tasu - ita kanta ziyarar na cikin kwas din da muke koyarwa kan nuna wariyar launin fata."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 1943: 'Yan nazi sun tsangwami Yahudawa

Labarai masu alaka