Kun san naman kwaɗo na da matuƙar daɗi kuwa?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku saurari rahoton Muhammad Annur Muhammad:

Kasuwancin kwadi na bunkasa a wasu yankuna na arewacin Najeriya inda masu cin kwadin ke cewa namansa tamkar na kaza ko kifi yake.

Daya daga cikin irin garuruwan da wannan sana'a yanzu ke bunkasa shi ne garin Chiromawa a jihar Kano da kuma Hadejia a jihar Jigawa, inda za ka ga 'yan kasuwa yawanci 'yan yankin kudu maso gabashin kasar da kuma jihar Benue da ke yankin arewa maso tsakiyar kasar na cuncurundo a kasuwannin da ake wannan hada-hada.

Sakataren dillalan kwadin a kasuwar ta Hadejia Aliyu Isama'il Mala, ya shaida wa BBC cewa, wannan kasuwancin nasu sai hamdala, duk da kallon banbarakwan da wasu ke musu kan sana'ar.

Masu wannan sana'a dai na korafin a kan rashin ware musu wuri mai kyau da zasu gudanar da wannan sana'a ta cinikin kwadi.

Image caption Ana bandar kwadin ne kafin a sayar

Ba dai duka nau'in kwadin ake sayar da su fa, misali nau'in kwado na tudu, ba a cin sa, saboda ya na da dafi, dan haka ba a sayar dashi.

Sauran kwadin da ba a kama su har ta kai da anyi bandarsu an sayar sun hadar da, Kurnu da Dan sanda da Bididdigi.

Yanzu dai kasuwancin kwadi na bunkasa, ganin yadda masunta da ma kabilu da dama ke shiga cikinsa.

Labarai masu alaka