Shin ina Nigeria ta dosa?

Wani mutm rike da tutar Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana yawan tabka muhawara a kan makomar kasar ta fuskar mulki da zamantakewa.

Yayin da wasu shugabannin al`umma da `yan siyasa ke bukatar a sauya fasalin zaman tarayyar da ake yi, saboda a ganin su ana tauye hakkin wasu bangarorin kasar, wasu kuma maganar ballewa suke yi.

A karon farko dai su ma al`umomin bangaren arewacin Najeriyar, wadanda ke kukan cewa ana musu kallon cima-zaune sun fara daga-murya suna cewa ya zama wajibi a sauya tsarin zaman da ake yi a kasar, idan ba haka ba, to kowa ya kama gabansa.

Shin ina Najeriyar ta dosa?

Batun sauya fasalin mulki da zama irin na tarayya a Najeriya dadadden al`amari ne, wanda masana ke cewa an fara maganarsa tun bayan hadi irin na baubawan-burmi da aka yi wa larduna uku na Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa, wato da lardin arewa da na kudu da kuma yammacin kasar sama da shekaru dari da suka wuce.

Haka dai aka yi ta tafiya ana dago batun daga lokaci zuwa lokaci, lamarin da ya yi sa wasu gwamnatoci, da suka hada da na soji da kuma na siyasa suka shirya wasu taruka da nufin tattaunawa a kan makomar kasa don samun mafita.

Rashin aiki ya karu a Nigeria

Nigeria: An yi gargadi kan saka hijabi

'Yan Nigeria na fama da yunwa - Saraki

Sai dai a dan tsakanin nan, an sake zafafa kiraye-kirayen sauya fasalin zama da mulkin Najeriyar.

Za ku iya sauraron rahoton musamman kan wannnan batun (sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don ku saurara)

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ina aka dosa game da batun sake fasalin Najeriya?

Kuma sabanin yadda aka saba jin wannan da`awa kan fito daga bakunan al`momin kudancin Najeriya, yanzu hatta wasu daga cikin mnyan `yan siyasa a arewacin Najeriya, irin su tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun fara bin sahu:

"Najeriya ba ta tafiya yadda ya kamata. Yadda aka fasalta kasar da tsarin mulki suna daga cikin dalilan da suka haddasa haka. Musamman ma tun shekarun 1960," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.

Ya ci gaba da cewa "gwamnatin tarayya ta girman sosai. Kuma ta tara iko mai yawa idan aka kwatanta da gwamnatocin jihohi. Akwai bukatar yin gyara ga wannan lamarin."

Labarai masu alaka