Boko Haram: An fara kewaye Jami'ar Maiduguri da ramuka

Rami Hakkin mallakar hoto Borno State Government
Image caption Shettima ya ce za a haka ramukan ne domin dakile duk wani yunkuri kai harin da za iya fuskanta a jami'ar nan gaba

Hukumomi a Najeriya sun fara aikin zagaye Jami'ar Maiduguri da ramuka don kare makarantar daga hare-haren kungiyar Boko Haram.

Sanarwar fara aikin wanda zai kai nisan kilomita 27 kuma zai ci naira miliyan 50, ta zo ne kwana guda bayan wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari jami'ar, inda suka kashe kansu da kuma wata ma'aikaciya.

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya sanar da aikin fara gina ramukan, yayin da ya kai ziyara jami'ar don duba ta'adin da maharan suka yi.

Gwamnan ya ce za a haka ramukan ne domin dakile duk wani yunkuri kai harin da za a kai jami'ar nan gaba.

Sojoji sun dakile harin kunar-bakin-wake a Borno

'Akwai 'yan Boko Haram a shugabannin Borno'

Borno na bukatar agajin gaggawa - MSF

Sai dai bai bayyana tsawon lokacin da za a kwashe ana aikin ba.

Har ila yau, shugaban Jami'ar, Aliyu Shugaba, ya ce sun gabatar da aikin ginin wata doguwar katanga wadda za ta kewaye jami'ar a wani mataki na kara kare jami'ar daga kowadanne irin hare-hare.

Jami'ar Maiduguri dai ta zama wani wuri da ke yawan fuskantar hare-haren 'yan Boko Haram a 'yan watannin nan.

Labarai masu alaka