Abba Kyari: 'Evans ya so ya gagari jami'an tsaron Nigeria'

Abba Kyari
Image caption An sa kyautar naira miliyan 30 ga duk wanda ya ba da bayanai da za su taimaka wajen kama Evans

Mataimakin Kwamishinan dan-sandan da ya jagoranci cafke madugun da ake zargi da garkuwa da jama'a da dama domin neman kudin fansa a Najeriya, ACP Abba Kyari, ya shaida wa BBC irin jan aikin da suka yi wajen cafke madugun.

A farkon wannan watan ne jami'an 'yan sanda a Legas suka yi nasarar kama Mista Chukwudi Onuwamadike wanda aka fi sani da sunan Evans bayan sun kwashe shekara bakwai suna farautarsa.

"Ya gagari dukannin jami'an tsaron Najeriya a tsawon kusan kimanin shekara bakwai," in ji Abba Kyari a wata hira da BBC.

An kama masu garkuwa da mutane a Kaduna

An sace tsohon ministan Najeriya, Amb Bagudu Hirse

Yadda 'manyan barayi' ke shirya fashi daga kurkuku - Abba Kyari

Har ila yau, Kyari ya ce Evans ya kwashe fiye da shekara 20 yana aikata laifuka a kasar.

"Ya kware sosai. Yana da layukan waya fiye da guda 100," in ji Kyari.

Sai dai har yanzu ba a gurfanar da Evans gaban kuliya ba domin jin ko zai amsa ko musanta laifukan da ake tuhumarsa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda kallon fina-finan bincike ya sa Abba Kyari ya zama gagarabadan dan sanda

Labarai masu alaka