An ba tsohon ministan Nigeria kyautar duniya kan noma

Akinwumi Adesina inspecting crops (Image: World Food Prize) Hakkin mallakar hoto World Food Prize
Image caption Dokta Adesina zai karbi dala 250,000 daga Gidauniyar Borlaug da ke Amurka

Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka Akinwumi Adesina ya samu kyauta kan muhimmiyar gudunmuwar da ya bayar wajen samar da abinci a duniya.

Dokta Adesina wanda shi ne tsohon ministan aikin gonar Najeriya, ya ce wadata miliyoyin manoma da iri da kuma takin zamani su ne muhimman abubuwan da za su kawo ci gaba ga aikin gona a nahiyar.

Ya kara da cewa kashi 98 cikin 100 na mutane miliyan 800 da ba sa samun wadataccen abinci suna Afirka ne.

A shekarar 1986 ne aka fara ba da kyautar abinci ta duniya don kara ingancin da kuma yawan abincin da ake nomawa a fadin duniya.

Dokta Adesina ya shaida wa BBC cewa yana alfahari da wannan kyautar da ya samu.

"A wajena, wannan kyautar ba ta kara daukaka sunana ba ce, tana nuni ne da bukatar bunkasa aikin gona a nahiyar Afirka," in ji shi.

Har ila yau, ya ce babban matsalar aikin gona a Afirka bai wuce karancin amfani da ake girbewa ba.

Hakkin mallakar hoto World Food Prize
Image caption An fara ba da kyautar ne a shekarar 1986

"Daya daga cikin abin da na dukufa yi shi ne kara kaimin ayyukanmu," in ji Adesina.

"Ka san ana iya samun lemun kwalba na Coca-Cola ko Pepsi a kusan kowane yankin karkara da ke nahiyar Afirka, to me sa ba a samun iri ko takin zamani haka?"

"Abin da ya sa hakan yake faruwa shi ne har yanzu tsoffin hanyoyin samar da iri muke amfani da su, wadanda suka dogara da gwamnati, kuma ba sa aiki yadda ya kamata."

"Hakan ya sa nake ganin cewa ya fi dacewa a tallafawa mazauna yankunan karkara don su rika sayar da taki da iri da kansu daga shaguna."

"Mun fara harkar dillancin kayan aikin gona kuma sun fara isa sassan Afirka da dama. Wannan tsarin na kawo irin da manoma suke bukata kusa da su kuma yana karfafa kasuwanci a karkara."

Dokta Norman E Borlaug wanda ya taba lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya, shi ne ya kirkiro kyautar aikin noman a shekarar 1986.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba