Salif Diao: Na so zama malamin makaranta ne

Salif
Image caption Diao ya kafa gidauniyar renon yara 'yan wasa a Senegal

Ya bar garinsu na Kédougou da ke kudancin kasar Senegal yayin da yake da shekara 13 don ya cimma burinsa na zama shahararren dan kwallon kafa.

Ya fara isa birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal wurin da a wasu lokuta yake kwana a wajen filin wasa kuma yake wanke kwanukan abincin sojoji don ya samu abincin da zai ci.

Hakan wani mataki ne wanda ya kai shi kulob din Liverpool, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya.

Bayan kimanin shekera 17 a matsayin shahararren dan wasa, Salif Diao, ya yi ritaya inda ya koma gida Senegal wurin da ya fara wasan.

Shaukin zama dan wasan kwallon kafa ya sa Diao ya yi watsi da karatunsa. Wanda hakan yake mai takaici yanzu.

"Abin babu sauki tun daga lokacin da nake da shekara 13 a duniya zuwa lokacin da na yi ritaya daga wasa," in ji Diao yayin da yake zaune a ofis dinsa da ke birnin Dakar.

"Na so na yi karatu ne a makarantar Prytanée Militair wadda tana daga cikin manyan makarantu a Senegal.

Amma hakan bai yiwu ba, kodayake na samu na yi wasan kwallon kafa. Ba abu ba ne mai sauki mutum ya hada kwallon kafa da kuma karatu a lokaci guda."

Diao bai samu ya yi karatu ba saboda yadda yake son zama shahararren dan wasan kwallon kafa.

Saboda yadda bai cimma burinsa na yin karatu, shi ya sa Diao ya kafa wata gidauniyar kimanin shekara uku da suka gabata.

Babban burin gidauniyar shi ne renon da yara 'yan wasan kwallon kafa da suke da ilimi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salif Diao yana cikin tawagar da ta wakilci Senegal a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2002

"Ina kaunar karatu saboda a yanzu ga inda muka samu kanmu, na yi ritaya, ban samu na yi karatu yanzu me zai yi ke nan," in ji shi.

Duk da cewa kwallon kafa ya ba shi duk abin da yake bukata a rayuwa, ya ce hanya daya da zai taimaki al'ummarsa ita ce ta samar wa yara abin da za su yi idan suka shiga mawuyacin hali.

"Idan ba ka da ilimi rayuwa tana da wuya, akwai wuya kuma musamma ma a Afirka, cikin 'yan wasa 1000 watakila guda daya ne zai zama shahararren dan wasa," in ji shi.

Image caption Diao ya ce yana da kyau a ba yara 'yan wasa ilimi ta yadda za su ji dadin tafiyar da al'amura yayin da suka samu daukaka

Duniyar wasan kwallon kafa ciki take da 'yan wasan da suka yi ritaya da bashin kudi a wuyansu.

Diao ya ce yana da kyau a ba yara 'yan wasa ilimi ta yadda za su ji dadin tafiyar da al'amura yayin da suka samu daukaka.

Ya ce kafin a karbi yaro a gidauniyarsa ta horar da 'yan wasa sai an tabbatar yana zuwa makaranta.

Gidauniyar tana samun gudummuwa daga tsofaffin kungiyoyin da ya yi wasa wato Liverpool da Stoke City.

Akwai cibiyoyin renon 'yan wasa kwallon kafa da yawa a kasar Senegal, amma cibiyar Diao ta gindaya sharadin cewa sai yaro ya gabatar da takardun da ke nuna cewa yana zuwa makaranta kafin a karbe shi.

"Muna abin da muka kware a kansa ne wato kwallon kafa. Amma yana da kyau mu ba ilimi muhimmanci sosai kuma abin da muke yi ke nan a gidauniyar," in ji Diao.

Idan aka dubi 'yan wasan Senegal kamarsu Sadio Mane da Idrissa Gana Gaye da suka samu daukaka, da wuya yara 'yan wasa masu taso su yarda cewa sanya karatu a gaba shi abin da ya dace.

"Suna kaunar wasan, suna so su yi suna kuma suna so su fita daga kangin talauci. Lokacin da nake yaro, so na yi na zama malamin makaranta ne amma yanzu so nake na zama mai horar da 'yan wasa ko koci. Saboda yadda suke da ikon cewa yara su tafi makaranta. Abin da ya sa ke nan muka kafa Gidauniyar Salif Diao - ko Cibiyar Wasanni, inda muke cewa yara idan suna so su zo nan, to wajibi ne su je makaranta," in ji Diao.

"Ya dace 'yan wasa masu tasowa su fahimci muhimmancin ilimi."

Yara suna son zama a gidauniyar. Suna sanya riguna wasa ne iri guda da na yara 'yan wasa da ke cibiyoyin horar da kwallon kafa na kungiyar Liverpool da Stoke City a Ingila.

Tsohon takwaran Diao, Stephen Gerrard ne yake ba su kyautar takalman da suke amfani da su.

Wasu daga cikin takalman ma suna dauke da sa hannunsa wanda wannan ba karamin abu ba ne ga yara 'yan wasa masu tasowa.

Labarai masu alaka