Na'urar ATM ta cika shekara 50 a duniya

ATM ya cika shekaru 50

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Na'urar ATM ta kawo sauyi a cinikayya a duniya

Shekaru 50 ke nan da fara amfani da na'urar fitar da kudi daga banki wato ATM Machine a duniya.

A ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 1967 ne wani wani banki a birnin Landan ne ya fara amfani da na'urar.

An samar da na'urar ne domin saukakawa mutane al'muransu musamman ta fuskar cire kudi idan bukatar gaggawa ta taso.

Ana dai amfani da na'urar ne wajen cire kudi, da sayen katin waya da biyan kudin makarantar yara ko biyan wani abu daban.

Hakazalika ana amfani da ATM din wajen tura kudi zuwa kowane bangare na duniya.

Kasar Koriya ta Kudu ita ce kasar da ta fi kasashen duniya yawan wannan na'urar inda ta ke da guda dubu 278, sai Australia da ta bi mata, sannan Japan.

A sahun kasashen nahiyar Afirka kuwa, Afirka ta Kudu ita ta fi sauran kasashen nahiyar Afirka yawanta.

Najeriya ma na daga cikin kasashen Afirkan da suke da yawan ATM.

Kiyasi ya nuna cewa, akwai na'urar guda miliyan uku a duniya.

Sharhi: Aisha Shariff Baffa

Na'urar tana da alfanu da kuma kalubale.

Daga cikin alfanun akwai samun kudi cikin sauki ba tare da ba ta lokaci ba; kuma ba sai mutum ya je banki ba.

Kalubalen kuwa shi ne, a wasu lokuta wannan na'ura na ba ta wa mutane rai ko lokaci, saboda a kan samu dogayen layin jama'a masu jiran su ciri kudi.

Wani lokacin kuma, zai nuna an kwashe maka kudi a asusun ajiyarka idan ka yi amfani da ita, amma ba tare da ya biya ka kudinka ba.

Ko kuma a wasu lokutan ya kan rikewa mutane katinsu banki, sai mutum ya sha wuya kafin katinsa ya dawo.