Masu amfani da Facebook sun kai biliyan biyu

Facebook logo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana sukar Facebook saboda gaza magance ta'addanci

Fiye da kashi daya cikin hudu na al'umar duniya na yin amfani da Facebook kowanne wata, a cewar shugaban shafin na sada zumunta.

Mark Zuckerberg ya wallafa a shafinsa cewa "Da safiyar nan masu amfani da Facebook suka kai mutum biliyan biyu".

Facebook ya kai wannan matsayi ne shekara 13 bayan Mr Zuckerberg ya bude shafin lokacin yana Jami'ar Harvard.

Ya watsar da karatunsa na Jami'a bayan ya bude shafin na Facebook.

A watan Oktoban 2012 ne shafin na intanet ya sanar da cewa masu amfani da shi sun kai biliyan daya, abin da ke nufin masu amfani da dandalin sun ninka cikin kusan shekara biyar.

Ci gaban da shafin Facebook ke samu ya zarta tunanin masu sharhi wadanda suka yi hasashen cewa zai samu koma baya tun lokacin da shafin Snapchat da ke gogayya da shi ya karbe wasu daga cikin masu mu'amala da shi.

A farkon wannan shekarar ne Facebook ya yi gargadin cewa kundin da yake samu ta hanyar tallace-tallace za su ragu.

Amma duk da haka burin Mr Zuckerberg bai ragu ba.

Ya shaida wa jaridar USA Today cewa ba su zuzuta samun masu amfani da shafin biliyan biyu ba saboda "bamu hada kowa da kowa da shafin ba".

"Abin da muke son yi shi ne kowa ya bude shafin Facebook," in ji shi.

Labarai masu alaka