Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela

Mutumin ya bayyana sunan sa Oscar Perez Hakkin mallakar hoto Instagram
Image caption Dan sandan da ya kai harin ya bayyana kan shi da suna Oscar Perez a shafin sa na Instagram

Wani jirgi mai saukar ungulu ya jefa bam a ginin kotun kolin Venezuela, a wani mataki da shugaba Nicolas Maduro ya kira fa aikin ta'addanci.

'Yan sanda sun ce wani jami'insu ne ya dauki jirgin helikofta, kana ya jefa gurneti ta sama kan kotun kolin kasar.

Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda jirgin ya tashi sama ya yi shawagi a sararin birnin Caracas, sannan ya saki gurneti.

An yi amanna da cewa jami'n dan sanda ya kwace jirgin ne, inda ya yi ta shawagi daga baya kuma sai aka ji karar fashewar gurnetin.

Babu dai wanda ya ji rauni ko ya rasa rai a harin ba.

Kasar dai na fama da rikice-rikicen siyasa da tattalin arziki, kusan kullum sai an yi boren kin jinin gwamnatin shugaba Nicolas Maduro tare da bukatar ya yi murabus.

Fiye da mutane 70 ne aka hallaka, a tashin hankalin da boren 1 ga watan Afirilu da ya wuce, kamar yadda ofishin babban mai shigar da kara ya bayyana.

Shugaba Maduro ya ce maharin da gurneti ya yi amfani, kuma ya sha alwashin jami'an tsaro za su kama masu hannu a kai harin.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Gwamnatin shugaba Maduro na fuskantar bore kusan kowacce rana

Shugaba Maduro ya shaida wa dandazon magoya bayan shi a wajen fadar gwamnatin kasar Miraflores ce wa ya bai wa jami'an tsaro umarnin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

''Nan ba da jimawa ba, za mu kama jami'in da ya tuka jirgin helikoftar, za mu kama duk wani mai hannu a harin ta'addancin da aka kai mana", inji shugaba Maduro.

Jami'in dan sandan ya wallafa wani hoton bidiyo a shafin Instagram, ya kira kan shi da suna Oscar Perez, wasu mutane da fuskarsu ke rufe da kyalle dauke da makamai sun kewaye shi.

Ya yi kira ga al'umar kasar su yaki mulkin kama karya.

Labarai masu alaka

Karin bayani