Tarayyar Turai ta ci Google tarar dala 2.7bn

Google Shopping Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Tallan da Google ke saka wa na kayansa na ture na sauran kamfanoni kasa

Hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai ta ci tarar kamfanin Google euro biliyan 2.42 (dala biliyan 2.7; fam biliyan 2.1) bayan da hukumar ta ce kamfanin ya ba kansa fifiko wajen tallata nasa kayan a saman shafukansa na samar da bayanai.

Wannan ita ce tara mafi girma da hukumar ta taba kakaba wa wani kamfanin da ake tuhuma da laifukan hana daidaiton cinikayya da wasu kamfanonin.

Hukuncin kuma ya umarci kamfanin na Google da ya daina halayen yi wa dokokin cinikayyar Tarayyar Turai karen tsaye cikin kwanaki 90, ko ya fuskanci karin matakai.

Kamfanin na Google na iya daukaka kara.

Amma idan Google ya kasa sauya halayyar tasa a cikin watanni uku, a na iya tilasta wa kamfanin da ya biya kashi 5 cikin dari na jimillar cinikin da uwar kamfanin na Google, watau Alphabet ke yi a dukkan fadin duniya.

Idan haka ta kasance, Google zai rika biyan dala miliyan 14 kenan a kowace rana.

"Abin da Google ya yi laifi ne a karkashin dokokin Turai," in ji Margrethe Vestager wacce ita ce kwamishinar samar da daidaito na kasuwanci a tsakanin kamfanoni dake Tarayyar Turai.

"Kamfanin ya hana sauran kamfanoni damar yin gasa da kuma samar da sabbin dabarun kasuwanci, kana kamfanin ya hana Tarayyar Turai amfana da zabin da irin wannan gasa ke samarwa."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
KALLI: Margrethe Vestager na bayyana tasirin halayyar kamfanin Google da yadda ya shafi kasuwanci

A nashi bangaren, kamfanin Google ya ce ai kamfanonin Amazon da eBay sun fi kowa amfana, kuma ya ki amincewa da tuhumar da a ke yi masa.

"Idan ka shiga intanet domin sayen kaya, kana bukatar samun bayanai game da kayan cikin hanzari da sauki," in ji wani kakakin kamfanin bayan da aka bayyana hukuncin.

"Ba mu amince da hukuncin da aka bayyana ba a yau. Za mu duba bayanan hukuncin, kana mu duba yiwuwar daukaka kara".

Gagarumin cigaba

Google kan nuna kayan da suka fi alaka da hotunansu, tare da sunayen shagunan da ake sayar da kayan.

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Idan aka duba bayanan kayan sayarwa da wayar hannu, na Google kan ture na sauran kamfanoni kasa

Binciken shekara bakwai

Hukumar ta Tarayyar Turai ta shafe kusan shekara bakwai tana binciken sashen kasuwanci na Google.

An gudanar da binciken ne sabili da wasu koke-koke da hukumar ta samu daga kamfanin Microsoft da wasu kamfanonin.

Kamfanin na Microsoft bai ce uffan ba bayan da aka bayyana wannan hukuncin,

Amma daya daga cikin masu koken, kamfanin Foundem ya yi maraba da hukuncin.

Shugaban Foundem, Shivaun Raff ya ce "Hana Google yin wadannan ababen da kuma tarar euro biliyan 2.42 da aka ci kamfanin zai yi tasiri wajen dakile irin wannan halayyar a gaba."

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba