Tsohon gwamnan Taraba Danbaba Danfulani Suntai ya rasu

Danbaba Suntai Hakkin mallakar hoto .
Image caption Marigayi Danbaba danfulani Suntai ya yi jinyan sama da shekera hudu bayan sakamakon hatsarin jirgin sama

Tsohon gwamnan jihar Taraba Danbaba Danfulani Suntai ya rasu yana da shekara 56, bayan ya shafe kusan shekara hudu yana jinyar hatsarin da yayi a cikin jirgin saman da yake tukawa.

Da yake tabbatar da mutuwar, tsohon kwamishinan watsa labaran jihar, Emamanuel Bello ya ce gwamnan ya rasu ranar Laraba.

Dan Fulani Suntai ya zama gwamnan jihar Taraba ne ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, kuma ya sake komawa kujerar a shekarar 2011, amman jirgin da yake tukawa da kansa ya yi hatsari ne ranar 25 ga watan Oktoban 2012, a kusa da birnin Yola dake jihar Adamawa.

Bayan ya samu kulawa a asibitoci a birnin Yola da Abuja, sai aka garzaya da shi Jamus da Amurka domin samun karin kulawa.

A wannan lokacin dai jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya ta shiga dambarwar siyasa saboda rashin lafiyar gwamnan, kuma bayan ya shafe wata goma yana jinya a kasar waje.

Danfulani Suntai ya dawo jihar ranar 23 ga wata Agustan shekarar 2013 a lokacin da magoya bayansa ke cewar ya na da lafiyar da zai iya ci gaba da mulkin jihar.

Bayan rikice-rikicen siyasa na makonni, an gano cewar gwamnan ba shi da lafiyar da zai iya ci gaba da mulkin jihar, kuma mataimakinsa Garba Umar ya ci gaba da zama mukaddashin gwamna kafin guguwar rikicin siyasar jihar ta cire shi.