Me yasa mata a India ke rufe fuska da kan shanu?

Wata mata sanye da kan saniya Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Hotunan sun janyo masa farin jini da kuma bakin jini

Wasu hotunan da aka dauka na matan da ke rufe fuskarsu da kan saniya a Indiya, ana tambayar ko shanu sun fi mata daraja a kasar ya ja hankali matuka a shafukan intanet a kasar. Lamarin da kuma ya janyo fushin wasu 'yan kasar a kan mai daukar hoton, wani matashi mai shekaru 23.

"Na damu matuka da abin da ke faruwa a kasata, ace an fi bai wa shanu muhimmanci fiye da mata, ta yadda idan aka yi wa mace fyade ko aka muzguna mata sai ya dauki mai tsawo lokaci kafin a bi mata hakkin ta, fiye da shanu da mabiya addinin Hindu ke bautawa." Sujatro Ghosh mai daukar hoto kuma mazaunin birnin Delhi ya shaida wa BBC.

Kasar ta indiya dai ta yi suna wajen aikata laifukan fyade a kan mata, inda wasu alkaluman gwamnati suka nuna cewa ana samun rahoton yi wa mace fyade a duk mintoci 15.

"A kan dauki shekarau ana irin wadannan shari'u a kotu kafin a hukunta wanda ya aikata laifin, amma idan aka ce batun ya shafi yanka sa ne , yanzu za ka yi mabiya addinin Hindu sun je sun kashe ko kuma sun yi wa wanda suke zargi da yanka wa dukan tsiya."

Wannan abin da ya yi a cewarsa "wata hanya ce ta nuna adawa" a kan tasirin da kungiyoyin kare shanu wadanada ke kara karfi tun bayan da jam'iyyar mabiya addinin Hindu ta BJP da firai minista Narendra Modi ta hau mulki a shekarar 2014.

"Abin da ya faru na kisan Dadri inda aka kashe [a lokacin da wasu mabiya 'yan Hindu suka kashe wani musulmi bisa zargin ya ci naman saniya ya kuma boye wani naman] da kuma wasu hare-hare na addini da a kan Musulmai da masu kare shanu ke kaiwa. " In ji Ghosh.

Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Mabiya addinin Hindu sun yi masa barazana
Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Wasu mata daga wasu sassan duniya na son suma su saka kan saniyar

A 'yan watannin baya-baya sa ya zamo dabbara da ake matukar kimarsa a India.

Jam'iyyar ta BJP ta jadadda cewa dabba ce mai tsarki saboda haka dole a kare ta. An haramta yanka shanu a jihohi da dama, inda aka sanya horo mai tsauri a kan duk wanda ya keta dokar, a yayin da kuma majalisa ke shirin yin wata dokar da zata kai ga hukuncin kisa ga wanda ya aikata laifin.

Sai dai cin naman saniya halal ne ga Musulmi da Kirista da miliyoyin mutane wadanda masu kare shanu ke kaiwa hare-hare.

An kashe kimanin mutum 12 a cikin shekaru biyun da suka wuce saboda shanu. Ana kai hari kan mutum ne da an rafa jin jita-jita kuma wasu muslmin ma an kai musu harii ne don sun dauko shanun domin a tatsi nono a jikinsu.

Ghosh wanda ya fito daga birnin Kolkata da ke arewacin kasar ya ce ya fara gano wannan "amarin mai cire da hadari ne na hada addini da siyasa" bayan ya komo Delhi a 'yan shekarun da suka wuce. Haka kuma a cewarsa "wannan abin da na yi wata hanya ce ta nuna adawa cikin ruwan sanyi da zai yi matukar tasiri".

A farkon wannan watan ne ya sani kan sa (ba na gaske ba) a wani shago a birnin New York, kuma bayan ya koma gida ne ya fara daukar hotunan mata a gaban wuraren bude ido da gine-ginen gwamnati da kan tituna, wasu a cikin gida ko kwale-kwale da ma jirgin kasa don nuna cewa "mata na fuskantar barazana a ko ina suke".

Ya ce "Na dauki hotuna mata daban-daban, inda na fara dauka daga birnin Delhi, babban birnin kasar kuma matattarar siyasa da addini har ma muhawara daga nan take farowa.

"Na dauki hoton farko a gaban mashigin India, inda masu yawon bude ido suka fi zuwa a Indiya. Sai na dauki wata mai tallar kayayyakin zayyana a kofar fadar shugaban kasa, wata kuma a cikin kwale-kwale a kan kogin Hooghly da ke Kolkata da gadar Howrah ta baya."

Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Mabiya addinin Hindu na daukar saniya wata abar bauta ce
Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Batun yanka saniya ya janyo asarar rayukan mutane, musamman musulmi a Indiya

Matan da suke cikin hotunansa wadanda ya sani ne saboda a cewarsa "batu ne mai sayar da jijiyar wuya, saboda haka zai yi wuya ka nemi wadda baka sani ba ta yi maka."

Lokacin da ya wallafa hotunan a dandalin sa da zumunta na Instagram a makonni biyu da suka wuce "an yaba sosai. kuma a makon farko ne miliyoyin mutane suka kalli hotunan, masu fatan alheri da ma mutanen da ban sani ba sun dinga yabawa."

Amma bayan kafafen yada labaran Indiya sun dauki labarin sun sanya shi a shafukansu na Facebook da Twitter, sannan ne kuma aka fara yi mini raddi.

"Wasu ma sun yi mini barazana wasu sun yi ta aibata ni , wasu ma na cewa ni da matan da ke cikin hotunan kamata yayi a kai mu masallacin Jama na Delhi a yanka mu kuma a bayar da namanmu ga mace 'yar jarida. Su ce za su so suga mahifiyata na kuka a kan gawata."

Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Hotunan na hannunka mai sanda ne ga jam'iyyar BJP mai mulki
Hakkin mallakar hoto Sujatro Ghosh
Image caption Hotunan na nuni da muhimmancin da aka baiwa sa fiye da matan da ake yi wa fyade a kasar

Wasu ma sun kai koke ne ga 'yan sandan Delhi, "suna zargin cewa ina yunkurin tayar da zaune tsaye saboda haka yakamata a kama ni".

Ghosh bai yi mamakin abin da aikinsa ya janyo masa ba, inda ya amsa cewa "hannunka mai sanda ya ke yi wa" jam'iyyar BJP.

"Na yi wani bayani ne da ya shafi siyasa, amma idan aka kalle shi da kyau za a ga fifikon da ake bai wa mabiya addinin Hindu, kuma dama can haka batun yake, sai dai a yanzu ya fi fitowa fili ne saboda su suke jan ragamar kasar tun shekaru biyu da suka wuce."

Barazanar da ake yi masa ba ta sa ya ji tsoro ba. "Bana wani fargaba domin na san abin da na yi zai yi tasiri mai kyau a kan al'umma da dama," In ji mai hoton.

Sai wani abu mai kyau da ya samu daga wannan abun shi ne mata da dama na kiransa daga sassa daban-daban na duniya suna yi masa tayin cewa su ma suna so su sanya kan saniyar a fuskarsu domin su shiga wannan kamfe din da yake yi.

Abin da ke nufin cewa kan san zai ci gaba da yin bulaguro.

Labarai masu alaka