Gungun 'yan Nigeria na hada baki da 'yan mafiya a Italiya

Wasu mata 'yan Afrika a Italiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu matan ana yaudararsu da cewa za a sama musu aikin yi ne a Italiya, amma idan suka je sai a tilasta musu shiga karuwanci

'Yan sanda a Italiya sun ce wani gungun masu aikata laifuka na 'yan Najeriya da ke zaune a birnin Sicily, na hada baki da kungiyoyin mafiya wajen sanya mata karuwanci da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Wata jami'a a cibiyar da ke nazarin ayyukan da suka kauce wa tsarin doka, a jami'ar Oxford da ke Ingila, Charlotte Baarda ta shaida wa shirin turanci na BBC, Newsday cewa kawancen kungiyoyin mafiyar da na 'yan Najeriya dadadden abu ne.

"A shekarun 1980 akwai matan Najeriya da dama da suka je Italiya saboda ana matukar bukatar masu aiki a cikin gida, sai dai daga bisani sun fahimci cewa anfi samun riba daga karuwanci kuma tun bayan nan ne matsalar karuwanci take ta karuwa."

Inda ta kara da cewa gungun masu aikata laifukan kamar kungiyar Black axe wadda ta samo asali a jami'oin da ke kudancin Najeriya, na bai wa kungiyoyin 'yan Mafiya na Italiya kudi domin a basu kariya a wuraren da suke aiki ko zama, amma a yanzu tasirin kungiyoyin 'yan mafiyan ya ragu bayan an garkame da dama daga cikin jagororinsu.

"Hakan yasa 'yan Najeriya ke iya kwace wurare ko yankunan da ake karuwanci ko safarar mutane cikin sauki ba tare da sun fuskanci turjiya ba, kuma su ne ke yanke hukunci a kan ko wa za'a bai wa damar shiga Italiya tare da ba da takardun izinin zama na bogi" In ji Charlotte.

Jami'ar ta yi karin haske a kan dalilan da yasa 'yan sandan Sicily suka kasa daukar mataki a kan gungun masu aikata laifukan na 'yan Najeriya.

"Yan sanda sun ce suna fuskantar matsala wajen samun bayanai ko kuma wadanda zasu iya tattara bayanan sirri da kuma masu tafinta, saboda yanki ne da kowa ya san kowa, mujami'a daya suke halarta saboda haka da wuya su samu hadin kai. Yayin da su kuma wadanda aka yi safararsu zuwa Italiyar ba zasu iya magana da 'yan sanda ba, saboda suna ganin rayuwarsu ta dogara kacokan ne a kan alumma. "

Sai dai ta ce a kasashe irinsu Belguim da Spaniya suna da jamian tsaro na musaman a kan yammacin Afrika, wadanda kan ziyarci wuraren da 'yan Najeriyar suke zaune, kuma su kan je har inda suke shan barasa domin su yi magana da mata 'yan Najeriya masu karuwanci.

Inda ta kara da cewa ko da yake suna samun bayanai a kan abin da ke faruwa, amma kuma abu ne mai sarkakiya.

Wasu bayanai dai sun nuna cewa jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta yi kaurin suna wajen safarar mata zuwa Italiya domin karuwanci.

Najeriya ta kafa hukuma ta musamman da ke yaki da safarar mutane ta NAPTIP, wadda ke yunkurin dakile matsalar.

Sai dai hukumar ta ce karfin kungiyoyin da abin ya shafa na kawo mummunan tsaiko wajen kawo karshen matsalar safarar mutane da kuma sanya mata karuwanci a kasashen ketare, musamman a kasar ta Italiya.