Qatar ta yi tur da kin amincewa da tattaunawa da Saudiyya ta yi

Ministan harkokin wajen Qatar, Sheikh Mohammed Bin Abdul Rahman ya shan hannu da sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ministan harkokin wajen Qatar ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka a Washington a ranar Talatar da ta gabata

Ministan harkokin wajen Qatar ya yi tur da kin amincewar da makwabtanta suka yi na a tattauna bukatun da suka mika wa kasarsa kafin su janye takunkumin rufe iyakokinsu na kasa da ruwa da kuma sama.

Sheikh Mohammed Al Thani ya ce matsayin da suka dauka "ya sabawa dokokin" dangantakar kasa da kasa.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce akwai yiwuwar Qatar ta fuskanci karin takunkumi daga abokan hamayyarta na kasashen Larabawa.

Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawan a Rasha, Omar Ghobash, ya shaida wa jaridar The Guardian cewa sabbin matakan za su hada da neman abokan cinikayyarsu su zabi wanda za su yi hulda da shi tsakanin su da Qatar.

Saudi Arabia da hadaddiyar daular larabawa da Bahrain da kuma Masar na zargin Qatar da tallafawa ta'addanci - zargin da ta musanta.

Kasashen sun mika wasu bukatu da suke son Qatar din ta yi, bukatun da ministan harkokin wajen Saudi Arabia ya ce "ba sa bukatar wata tattaunawa" a ranar Talatar da ta gabata.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Qatar za ta dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa duniya ta duniya a shekarar 2022

Takunkumin dai ya shafi Qatar, kasar da ke da arzikin iskar gas wadda ta dogara da shigo da abubuwan bukatu na rayuwa daga kasashen waje ga jama'a miliyan biyu da dubu dari bakwai.

A ranar juma'a ne kasashen Larabawan hudu suka mikawa Qatar bukatun 13 da suka hada da rufe gidan talabijin na Al Jazeera da rufe sansanin sojinta da ke Turkiyya da yanke hulda da kungiyar 'yan uwa Musulmi da kuma rage karfin dangantakarta da kasar Iran.

Labarai masu alaka

Karin bayani