Obama da iyalansa na shakatawa a Indonesia

Barack Obama da 'yarsa Malia Obama sun kai ziyara wurin bauta na Borobudur da ke birnin Magelang Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mista Obama da 'yarsa Malia sun yi wasanni a lokacin hutun na su.

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama da iyalansa sun tafi hutu kasar Indonesia, inda suke ta kai ziyarar fitattun wurare a kasar ciki har da wuraren bauta.

Obama da mai dakinsa da kuma 'ya'yansa mata biyu, sun fara sauka ne a tsuburin Bali, daga bisani kuma suka kai ziyara wurin bautar addinin Budda da ke Java a ranar Laraba.

Obama dai sanannen mutum ne a kasar, ya kuma samu tarba ta musamman daga mutane inda suka yi ta daukar su hotuna.

A zamanin kuruciyarsa, Obama ya taba zama a Indonesia na tsahon shekara hudu.

Ya fara zama a kasar ya na da shekara shida, lokacin da mahaifiyarsa ta auri wani dan Indonesia bayan mutuwar auren ta da mahaifinsa dan kasar Kenya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Obama ya kai ziyara wurin bautar mabiya addinin Budda, mai dadadden tarihi
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Ya'yan shugaban ba su raka mahaifinsu da mahaifiyarsu Indonesia ba a shekarar 2010, lokacin da suka kai ziayara.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masoyan tsohon shugaban kan taru da jinjina masa, ya yin da a lokuta irin wannan ake kara matakan tsaro dan bashi kariya

A shekarar 2010 ya sake dawowa kasar tare da mai dakinsa Michelle, a matsayin shugaban kasar Amurka.

Bayan kammala wa'dinsa a matsayin shugaban Amurka, 'ya'yansa na yawan yi wa iyayensu rakiya idan za su yi balaguro.

Haka kuma a tafe suke da jami'an tsaro, domin ba su kariya.

A ranar Juma'a ne ake sa ran Mista Obama zai gana da shugaba Joko Widodo na Indonesia, a fadar gwamnatin kasar da ke kudancin birnin Jakarta.

Labarai masu alaka