Habasha ta bukaci Saudiyya ta kara wa'adin afuwa ga baki 'yan ci-rani

'Yan Habasha kenan a lokacin da suka sauka a filin jirgin saman Bole da ke birnin Addis Ababa a ranar 10 ga watan Disambar 2013 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban Habashawa ne ke zuwa Saudiyya da nufin samun ayyukan yi

Gwamnatin Saudiyya ta bai wa dubban bakin 'yan ci-rani da suka shigo kasar ba bisa ka'ida ba, wa'adin kwana 90, kamar yadda hukumomin Ethiopia suka bayyana.

Ministan sadarwar kasar Negeri Lencho ya shaidawa BBC gwamnatin Habasha ta roki hukumomin Saudiyya su karawa 'yan ciranin wa'adin.

Ya kara da cewa fiye da 'yan kasar 45,000 ne suka dawo gida, kuma har yanzu akwai wasu dubban da su ke jiran lokacin komawa kasarsu.

Mutanen Habasha dai na ayyukan da suka shafi gine-gine, da aikatau a gidajen larabawa.

Mista Negeri ya ce gwamnatinsu na jiran amsar da Saudiyya za ta ba su, wanda ya ke fatan za ta zamo mai armashi.

A watan Maris da ya wuce, ministan cikin gidan Saudiyya yarima Mohammed bin Naif bin Abdulaziz,ya sanar da yi wa 'yan cirani mazauna kasar ba bisa ka'ida ba an ba su wa'adin watanni uku su fice daga Saudiyyar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ba za ta hukunta wadanda suka kawo 'yan ciranin ba, da gidaje ko kamfanonin da suka dauke su aiki, duk da cewa sun take dokar kasar ta hanyar zama cikin ta ba tare da takardar shaida zaman kasa ba wato Iqama.

A shekarar 2013 ma hukumomin Saudiyyar sun yi irin wannan afuwar, amma duk wanda aka samu da ketare wa'adin zai fuskanci fushin hukuma, da suka hada da zaman gidan kaso da biyan tara.

Haka kuma, a wannan lokacin an hallaka 'yan Habasha da dama a wata zanga-zanga da suka yi taho mu gama da 'yan sanda, lokacin da gwamnati ta sha alwashin tasa keyarsu kasashen su.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan cirani a motocin safa-safa za a fice da su daga kasar Saudiyya shekarar 2013

Mista Negeri ya kuma ce mutane sun yi hasashen daman Saudiyya ka iya tasa keyar 'yan ciranin kasashen su bayan kammala azumin watan Ramadan.

A bangare guda kuma hukumomin Habasha sun sanar da ware wasu kudade dan tarbar 'yan kasar da za su dawo gida, da sama musu muhalli.

Labarai masu alaka