Dalilin barin jirgin Buhari a filin jirgin sama na London

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ki cewa uffan kan batun rikicin na APC

Kakakin shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa jirgin saman shugaban kasar na ajiye a filin jirgin sama na Stanstead dake birnin Landan, tun da ya kai shugaba Buharin Ingila domin neman lafiya.

Amma ya musanta cewa ana kashe makudan kudaden wajen biyan kudin ajiyar jirgin.

Garba Shehu, wanda shi ne kakakin shugaba Buhari ya bayyan haka ne a cikin wasu bayanai da ya raba wa maneman labarai, inda ya kara da cewa "Abu ne mai muhimmanci a gane cewa domin dalilan tsaro, da na diflomasiya, da martaba, babu wani shugaban kasa a duniya da yake tafiya wata kasa ba tare da an tabbatar da an samar da jirgin komawarsa gida ba cikin gaggawa, idan hakan ya zama wajibi".

Ya kuma kara da cewa "Jami'an sojin kasar nan ba zasu bar aikinsu na kula da babban kwamandan sojojin Najeriya ba a duk irin halin da ya sami kan shi." Inda kuma ya ce "Wannan shi ne tsarin da ake bi a kowace kasa ta duniyar nan".

Kakakin ya karyata masu sukar gwamnatin a shafukan sada zumunta, inda suke cewa gwamnatin na kashe kimanin dalar Amurka 4,000 a matsayin kudin ajiyar jirgin shugaban a kowace rana.

"Wadannan alkaluman babu gaskiya a cikinsu. An tabbatar mana cewa a kan ba shugabannin kasashe wani farashi na musamman wanda bai kai na 'yan kasuwa ba."in ji kakakin.

Ya kara da cewa "Kudin da ake cajin Najeriya ba zai wuce fam 1,000 ba a kowan yini, abin da bai wuce kwatan wanda ake bazawa ba"

Idan ba a manta ba, mutane sun yi ta baza labaran irin kudaden da gwamnatin Najeriya ke kashewa wajen ajiyar jirgin saman shugaba Buhari wanda ya shafe kwanaki 50 a yau yana jinya a birnin Landan.