Nigeria za ta fara fitar da doya zuwa Birtaniya

Yam Hakkin mallakar hoto Pascal Deloche /GODONG
Image caption Najeriya tana neman kara hanyoyin samun kudaden kasashen waje

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da fara fitar da doya daga kasar zuwa Birtaniya domin samarwa kasar karin kudin kasashen waje.

A ranar Alhamis ne aka kaddamar da fitar da doyar, da yawanta ya kai tan 72.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da shirin, ministan noma na Najeriya, Audu Ogbeh, ya ce abun kunya ne a ce Najeriya da take samar da kashi 61 cikin 100 na doya a duniya, amma ba a samu doyarta a kasashen waje.

Mista Ogbe ya ce Ghana tana samun kusan dala biliyan hudu daga doya a ko wace shekara, yana mai karawa da cewar dole Najeriya ta fitar da dukkan abun da kasashen waje suke nema, domin ta kara hanyoyin samun kudaden kasashen waje.

Ya ce gwamnatin tana shirin kera sabuwar garma da zata iya yin kunyar doya da yawa a lokaci kadan, domin kasar ta kara yawan doyar da take nomawa.

Amma wasu 'yan kasar sun fara nuna fargaba game da shirin, suna cewa shirin zai sa doya ya kara tsada a kasar.

To sai dai ministan noman kasar ya ce shirin ba zai kawo tamowa ba, domin kasar ba ta da matsalar karancin abinci, kuma ana asarar doya mai yawa saboda rashin wuraren adana ta.

Ya ce gwamnatin kasar ta ce za ta samar da na'urorn adana doyar.