Da me za ka tuna ɗan ƙwallon Nigeria Nwankwo Kanu?

Kanu Nwankwo
Image caption Gidauniyar kula da masu ciwon zuciya ta Kanu tana tallafa wa yara masu larurar ciwon zuciya

Ɗaya ne daga cikin fitattun 'yan wasan ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka, Nwankwo Kanu na Najeriya ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da ƙasar ta samu yayin gasar Olympics da aka yi a Atlanta cikin 1996.

Ya kuma lashe kusan duk kofunan da ake da su a wasan ƙwallon ƙafa, ko da yake, ya fi son a tuna shi da ceton rai fiye da ƙwallon ƙafa.

Watanni kaɗan bayan ya ci lambar zinariya a gasar Olympics, ciwon zuciya ya tilasta masa barin ƙwallo har tsawon wata tara.

Lamarin da ya sanya shi kafa gidauniyarsa ta kula da masu ciwon zuciya a shekara ta 2000, inda ya fi mayar da hankalinsa.

Kanu ya ce rasuwar ɗan wasan ƙasar Ivory Coast a China ya kamata ya wayar da kan mutane game hatsarin da ke tattare da cutukan zuciya.

Tiote wanda ya mutu yana da shekara 30 a duniya, bayan ya yanke jiki ya faɗi lokacin da yake atisaye a China inda ya taka wa ƙungiyar kwallon kafa ta Beijing Enterprises leda.

Kanu, wanda shi ma ya yi fama da ciwon zuciya a lokacin da yake wasa, ya ce lokaci ya yi da za a cikin filin wasa da wajensa. Dan Najeriyan bai buga wasa ba har tsawon wata tara bayan likitocin Inter Milan sun gano wata tawaya a zuciyarsa.

Kanu ya ce: "Labarin rasuwar Tiote ba mai dadi ba ne. Wannan ba karon farko kenan ba. Mun rasa Marc-Vivien Foe. Ya mutu, kuma babu abin da aka yi. Tiote ya riga mu gidan gaskiya , kuma babu abin da ake yi a kansa."

Tiote ya shiga jerin 'yan wasan Afirka da suka mutu a cikin filin kwallo sakamakon ciwon zuciya.

Tsohon dan wasan Ajax Amsterdam da Inter Milan da Arsenal da kuma Portsmouth FC ya ce zai yi iyakar kokarinsa wajen magance matsalar. Yana kokarin gina asibitin ciwon zuciya a kan dala miliyan 17 a Abujan Najeriya.

Baya ga haka yana son gina asibitoci irin wannan a wasu kasashen Afirka- daya a gabashin Afirka, daya arewaci, daya kuma a kudancin nahiyar.

Ya ce "Ina magana da abokaina saboda mu iya yin wani abu domin mu sake wayar da kan jama'a, mu yi kokarin taimaka wa yara a Afirka.

Mutum daya ba zai iya yin komai da komai ba. Abin da ya faru da Tiote darasi ne ga dukkanmu. Dole a ci gaba da magana a kai.

Ba za mu iya bari haka ta ci gaba da faruwa ba, domin matsalar babba ce."Kasancewarsa, dogo maras jiki da zura kwallonsa mai hatsari da kuma dabarunsa, Tiote ya fita daban a cikin sauran 'yan kwallo.

Kanu ya fi mayar da hankali kan batun cututtukan zuciya ne yanzu.

Abia Onyebuchi, jagoran gidauniyar kula da masu cututtukan zuciya ta Kanu, ya tuna lokacin da Kanu ya fara mayar da hankali a kan batun.

Abia Onyebuchi ya ce : "An yi masa aiki a Cleveland Ohio a jihar Ohio da ke Amurka. matashin ya dawo, lokacin da Najeriya ta lashe lambar zinariya a gasar kwallon kafa ta Olympics kenan, kwatsam sai aka ji yana da matsalar ciwon zuciya kuma mai yiyuwa ne ba zai sake taka leda ba."

Ya kara da cewar : " 'Yan Najeriya sun taimaka masa da addu'a. Da ya dawo ya ce hanya daya da zai bi ya saka wa abin da 'yan najeriya da 'yan Afirka suka yi masa wajen nuna masa goyon baya a lokacin da yake fama da wannan ifti'ila'i, shi ne kafa gidauniyar kula da masu ciwon zuciya ta Kanu."

An yi wa Kanu tiyata a shekarar 1996 domin kawar da wata cuta da aka gano lokacin gwaje-gwaje a kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan.

A lokacin ya samu duniya domin yana cikin murnar lashe zinariya a gasar Olympics da kuma komawa Inter Milan daga Ajax Amsterdam.

Labarin matsalar zuciya ya durkusar da kwallonsa.

Wannan lamarin ne ya sauya rayuwarsa har abada, abin da ya sa shi kafa gidauniyar zuciya irin wannan a shekara ta 2000.

Ya hadu da wakilin BBC a London kuma ya yi karin bayani game da abun da yake shirin yi.

Kanu ya ce :"Burinmu shi ne mu gina asibiti daya a Najeriya da kuma kasashen Afirka hudu. Matsalar dai ta kudi ce.

Amman idan muka samu kudin ko kuma muka gina asibitin, zai taimaka matuka saboda a yanzu haka muna kai yara Indiya ne kuma yana da tsada sosai. Yana ba mu wahala.

Saboda haka muna kokarin duba yiwuwar daukar mataki ta hanyar gina asibiti ga yara marasa galihu masu matsalar ciwon zuciya."

Gidauniyarsa tana son taimaka wa matasan Afirka da ke fama da cutukan zuciya iri-iri.

Kawo yanzu dai gidauniyar ta yi nasarar yi wa mutum 538 tiyata a Ingila da Indiya da kuma Isra'ila.

Karo uku ne kawai ba a yi nasara ba. Wani dalibi a jami'ar Legas, Enitan Adesola, daya ne daga cikin mutane biyu da suka fara cin gajiyar aikin.

"Dole ne in gode masa domin daukar wani babban mataki na taimaka mini saboda ba kasafai ake taimaka wa wanda ba a sani ba. Tamkar Uba yake a gare ni. Ya taimaka mini matuka. Na gode sosai, in ji Enitan Adesola.

Irin wadannan kalaman ne suka sa Kanu yake son ci gaba da taimakawa.

Kanu: "Abu mai kyau ne, idan ka ga mutane suna zuwa suna cewa sun gode. In ka tambaye su me ya sa, sai su ce suna cikin wadanda suka ci gajiyar gidauniyar ciwon zuciya ta Kanu ne. Wannan babban abu ne. Ya fi lashe duk wata gasa dadi."

Daga ofishoshin gidauniyar da ke Surulere ta Legas, inda a wasu lokuta injin janareta yake samar da wuta, Kanu yana son ci gaba da burinsa na ceton rayuka, kuma yana hada kai da gidauniyar Nelson Mandela a Afirka ta Kudu domin tara kudin gina asibitin ciwon zuciya.

Abia Onyebuchi, jagoran gidauniyar shi yake shirya gangamin tara gudunmawar kafa asibitin.

Abia Onyebuchi: "Gwamnatin tarayya ta ba mu wani fili a Abuja domin gina asibitin.

In Allah Ya yarda, fitattun 'yan wasan kwallon kafa na Afirka za su buga wasan sada zumunci don gidauniyar zuciya ta Kanu da kuma gidauniyar Nelson Mandela.

Abu ne namu na Afirka. Abu ne da muke yi domin kanmu saboda samun sauki."

Labarai masu alaka