An gurfanar da wani kan daukar bidiyon mace tana tatsar ruwan nono

bilinboti Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Ana kara nuna bukatar kamfanoni su samar da wurin da mata za su iya shayar da jariransu

Wata mata ta kai karar wani abokin aikinta kotu, bisa zarginsa da daukar hoton bidiyonta a asirce tana tatsar ruwan nono, a wajen aiki a kasar Afrika ta Kudu.

An zargi mutumin wanda jami'ar Cape Town ta dakatar, da sanya bidiyon da ke watsa abu kai tsaye a wani daki a jami'ar a ranar 13 ga watan Yuni.

Matar ta rubuta a shafinta na intanet cewa ta fusata da ganin cewa samar wa jaririnta abinci ya zamo "wata hanya mara ma'ana ta samun biyan bukata".

An gurfanar da mutumin kuma tuni aka fara bincike a kan lamarin.

'Yan sandan yammacin Cape sun tabbatar da cewa an fara binciken ma'aikacin jami'ar mai shekara 38 a duniya.

Kafafen yada labarai na kasar sun bayyana yadda matar da yada "bacin ranta" a kan lamarin, cewa ta dauka tana wani daki ne a 'kebe inda babu kowa kuma a kulle' sai ta fara tatsar ruwan nonon kafin ta farga cewa ana daukar hoton bidiyonta.

Ta ce "Abin haushi ne ainun ace muna rayuwa a duniyar da iyaye mata ta duk yadda muka zabi mu shayar da jariranmu, sai an samu wani ya ci mutuncinsu saboda suna da rauni."

A fadin duniya dai ana nuna bukatar ma'aikatu su samar da kebantaccen wurin da iyaye mata za su iya shayar da jariransu.

Labarai masu alaka

Karin bayani