A Niger mutum hudu sun mutu a hari kan sansanin 'yan gudun hijira

Wasu jami'an tsaro a mota Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yankin Diffa na karkashin dokar ta-baci

A jamhuriyyar Nijar, rahotanni daga jihar Diffa na cewa wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari a sansanin 'yan gudun hijiran Nigeria da ke garin Kablewa cikin gundumar Gigmi.

Mutane hudu ne dai suka halaka ciki har da 'yan kunar bakin waken mata biyu a ranar Laraba da daddare, yayin da wasu mutum goma kuma suka jikkata.

Wasu rahoatnni sun ce masu kunar bakin wake hudu ne suka je sansanin, maza biyu da mata biyu.

Sai dai mazan sun labe ne daga nesa, inda suka ruga zuwa yankin tafkin Chadi bayan matan sun tayar da bama-baman da ke jikinsu.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun samu shiga sansanin ne duk da cewa akwai jami'an tsaro a wurin, ko da yake a yanzu an kara karfafa matakan tsaro a ciki da wajen sansanin bayan harin.

Harin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kungiyar tarayyar Afrika and shugaban kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde ya yi kira ga kasashen Afrika su dogara da kansu wajen yaki da yan ta'adda a yankin Sahel.

Shugaban ya bukaci kasashen nahiyar da su yunkura su samar da sojojin da za su yi yaki da ta'addanci, ganin kungiyar rundunar Majalisar Dinkin Duniya, MUNISMA da ke Mali ba ta tabuka wani abin a zo a gani ba.

Mista Conde ya furta wannan maganar ce a yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar Chadi a ranar Laraba.

Ko da yake kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin

Sai dai kasashen Najeriya, Nijar da Kamaru na daga cikin kasashen da kungiyar Boko Haram take yawan kai hare-hare a yankin tafkin Chadi.

Tuni dai aka kafa wata rundunar hadin guiwa ta kasashen yankin tafkin Chadi da ke yaki da kungiyar Boko Haram.