Mutanen Taraba 3000 na gudun hijira a Kamaru

Wata 'yar gudun hijira a Kamaru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dama akwai dubban 'yan Najeriya da ke zaman gudun hijira a Kamaru

Wasu rahotanni na cewa sassan jamhuriyyar Kamaru da suka yi iyaka da jihar Taraba a Najeriya na karbar wasu sabbin dubban 'yan gudun hijira.

Akasarin 'yan gudun hijiran Fulani ne makiyaya maza da mata da kuma kananan yara, wadanda suke ficewa sakamakon rikici tsakaninsu da Mambilawa a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba a Najeriya.

An kiyasta cewa kusan 'yan gudun hijira 3,000 ne suka shiga wasu garuruwa kamar Mayo-Darle a Lardin Adamawan, inda aka sauke a makarantun boko.

Rahotanni daga Mayo-Darle a Lardin Adamawan Kamaru na cewa sabbin 'yan gudun hijira daga Jihar Taraba a Najeriya na kwararowa domin neman mafaka.

Yayin da wasu 'yan gudun jihar kuma suka sauka a wajen dangi da 'yan uwansu da ke Kamaru.

Haka kuma akwai rahotannin da ke cewa akwai wasu dumbin 'yan gudun hijirar da ke samun kulawa a asibitin Fanso sakamakon raunukan da suka ji.

Dama can kasar ta Kamaru na kula da dubban 'yan Najeriya da suka tserewa rikicin Boko Haram.