Evans ya shigar da 'yan sandan Nigeria kara a Kotu

speton 'yan sandan Nigeria Hakkin mallakar hoto Idris facebook
Image caption 'Yan sandan Najeriya sun shafe shekaru bakwai suna farautar Evans

Mutumin da ake zargin shi ne madugun satar mutane a Najeriya, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya shigar da karar 'yan sanda a kotu.

Evans na zargin sufeton janar na 'yan sandan kasar, Ibrahim Idris da kuma wasu jami'an 'yan sanda uku a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Lagos, inda yake zargin 'yan sandan da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Lauyan mutumin ne ya shigar da karar a madadin Evans, inda ya nemi kotu da sa wadanda yake karar su gurfanar da shi ba tare da bata lokaci ba.

Karar wadda aka shigar a makon jiya ta bukaci kotu ta sa 'yan sanda su tuhume shi idan suna zarginsa da wani laifi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

A farkon wannan watan na Yuni ne dai aka cafke Evans tare da wasu mutum shida da ake zarginsu da ayyukan satar mutane.

Kuma tun a shekarar 2013 ne dai aka yi yekuwar nemansa ruwa a jallo.

Sai dai kakakin 'yan sanda, Jimoh Moshood ya shaida wa BBC cewa sun samu umarnin wata kotun tarayya wadda ta ba su damar tsare Evans har sai sun kammala bincike a kansu.

Rundunar 'yan sandan Ghana ma ta sanar da kaddamar da bincike a kan Evans din wanda ke da fasfo na kasar, haka kuma iyalinsa ma na zaune ne a Ghanan.