Jirgi mai samar da intanet ya yi tashi na biyu

Aquilla Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Manufar jirgin wanda ba ya gudu sosai shi ne samar da tsayayyen layin intanet ga yankin da yake shawagi a cikinsa na tsawon lokaci.

Facebook ya kammala gwada wani jirgin da ya ƙera maras matuƙi da ke amfani da hasken rana a karo na biyu, don samar da intanet ga yankuna masu rata na duniya.

Jirgin - wanda aka yi wa laƙabin Aquila - ya tashi tsawon sa'a ɗaya da minti 46 a cikin yankin Arizona na Amurka.

A gwajin da Aquila ya yi na farko cikin bazarar da ta gabata, iska mai ƙarfi ta jigata shi, inda ya faɗo a lokacin sauka.

Wannan karo, jirgin ya luluƙa sama tsawon ƙafa 3,000, ƙasa da burin kamfanin Facebook na ƙafa 60,000 a sararin samaniya.

Kamfanin sada zumuntar na da burin samar da kwambar jiragensa marasa matuƙa, waɗanda yake so, su riƙa sadarwa da juna tare da yin karakaina a sararin samaniya tsawon watanni idan sun tashi.

Facebook tun da farko ya bayyana gwajin jirgin na watan Yunin 2016 a matsayin wanda ya yi nasara, amma daga baya ya amsa cewa ya faɗo a lokacin sauka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mark Zuckerberg ya ce yana jin nana gaba za a iya samun dubban irin waɗannan jirage suna karakaina a sararin samaniya don wadata layin intanet a cikin rahusa ga biliyoyin mutane.

Ayarin jami'an da ke kula da harkokin jirgin sun ɗauki hoton bidiyon gwajinsa na biyu a lokacin da yake sauka inda suka buga a shafin intanet.

Aquila - wanda ke da faɗin fuka-fukan jirgin Boeing 737 - wani ɓangare ne na shirin Facebook don haɗa duniya da layin intanet.

A wannan mako, Facebook ya sanar cewa masu amfani da shafinsa sun kai mutum biliyan biyu, fiye da rubu'in yawan mutanen duniya.

Labarai masu alaka